‘Yar Najeriya Ngozi Okonjo-Iweala ta shiga sahun mutum 100 da suka fi karfi a Duniya

‘Yar Najeriya Ngozi Okonjo-Iweala ta shiga sahun mutum 100 da suka fi karfi a Duniya

  • Dr. Ngozi Okonjo-Iweala tana cikin mutanen da suka fi karfi a fadin Duniya
  • Mujallar Times ta bayyana haka a sabon jerin da ta fitar na shekarar 2021
  • Tsohuwar Ministar Najeriyar ta zama macen farko da ta rike kujerar WTO

Mujallar Times tace Dareka Janar ta kungiyar kasuwanci na Duniya, Ngozi Okonjo-Iweala, tana cikin jerin mutane 100 da suka fi tasiri a fadin Duniya.

Duk shekara wannan mujalla ta kasar waje ta kan fito da jerin manyan mutanen da suka fi karfin fada-a-ji da tasiri saboda aiki ko mukaman da suke kai.

“Ana zakulo mutanen da fikirarsu, baiwarsu da misalinsu ya kawo sauyi a Duniyar da muke ciki.”

Jaridar The Cable tace a jerin da aka fitar na ranar Laraba, 15 ga watan Satumba, 2021, akwai kasurguman ‘yan kasuwa, ‘yan wasa da kuma jagorori.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan bindiga sun bindige shugaban cocin Anglika har lahira a Imo

Ngozi Okonjo-Iweala ta yi zarra

Dr. Ngozi Okonjo-Iweala wanda a watan Maris ta zama macen farko da ta hau kujerar WTO tana cikin daidaikun bakaken matan da sunan ta ya fito a jerin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wannan jerin yana kunshe da mutane irinsu shugaban Amurka Joe Biden da mataimakiyarsa, Kamala Harris, da kuma shugaban kasar Sin, Xi Jinping.

Ngozi Okonjo Iweala
Dr. Ngozi Okonjo Iweala Hoto: www.ladunliadinews.com
Asali: UGC

Har wa yau sunan Firayim Ministan Indiya, Narendra Modi, ya samu shiga jerin shekarar bana.

Harry da Meghan Markle sun yabi Okonjo-Iweala

Yariman Birtaniya Prince Harry da Meghan Markle wanda suna cikin jerin sun yaba wa aikin da Okonjo-Iweala ta ke yia WTO. A cewarsu ta san kan aiki.

“Duk da kalubale, ta san yadda za ta shawo kan abubuwa – Ko a cikin wadand ba su yarda da ita ba – Ta kan yi wannan da murmushi, babu tada hankali.”

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun kai farmaki gidan yari, sun saki fursunoni 240 sannan suka kashe sojoji a Kogi

Jaridar Punch tace tsohuwar Ministar tattalin arzikin ta gode wa Yarima Harry da Meghan Markle a game da irin kalaman masu dadi da suka fada a kanta.

Dr. Okonjo-Iweala ce kadai mutumiyar Najeriya da sunan ta ya shiga TIME 100 na bana.

Za ayi taron majalisar dinkin Duniya

An samu labari cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai hau mimbarin majalisar dinkin Duniya a birnin New York, zai yi magana a taron shekarar nan.

Buhari zai tofa albarkaci bakinsa tare da wasu shugabannin Duniya irinsu Joe Biden. Shugaban Najeriyar zai yi magana ne a ranar 24 ga watan Satumba, 2021.

Asali: Legit.ng

Online view pixel