An zabi Shugaban Najeriya Buhari ya yi jawabi a zauren Majalisar dinkin Duniya

An zabi Shugaban Najeriya Buhari ya yi jawabi a zauren Majalisar dinkin Duniya

  • Muhammadu Buhari yana cikin masu jawabi a taron majalisar dinkin Duniya
  • Buhari zai yi magana a taron wannan shekarar ne a ranar 24 ga watan Satumba
  • Shugaban Najeriyar ne mutum na biyu da zai yi jawabi a rana ta hudu a taron

U.S.A - Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi jawabi a taro na 76 na majalisar dinkin Duniya da za ayi a hedikwatarta da ke birnin New York, Amurka.

Jaridar The Nation ta bayyana cewa Mai girma Muhammadu Buhari yana cikin wadanda aka zaba su yi magana a zauren a ranar 24 ga watan Satumba, 2021.

Hukumar dillacin labarai na kasa tace shugaban Najeriyar shi ne mutum na biyu da zai yi jawabi a rana ta hudu na wannan taro da zai gudana a kasar Amurka.

Rahoton ya tabbatar da cewa Muhammadu Buhari shi ne mutum na biyu da za a saurara a ranar. Ana sa rai Buhari zai yi magana ne a ranar Juma’a da safe.

Kara karanta wannan

Binciko Gaskiya: Da gaske ne DSS sun kama telan Buhari da ya yi masa dinkin Imo?

Da safe za ayi jawabin, amma a agogon Najeriya, za a saurari shugaban kasar ne da karfe 2:00 na rana.

Shugaban Najeriya Buhari
Buhari a taron UN Hoto: news.un.org
Asali: UGC

Joe Biden zai halarci taron farko

Shugaban da zai fara magana a taron wannan karo shi ne na kasar Brazil, Jair Bolsonaro. Kamar yadda dai aka saba, daga shi sai shugaba Amurka, Joe Biden.

Shugabannin kasashe 80 ne za su yi magana a taron majalisar dinkin Duniyan. Wasu daga ciki za suyi magana a dauka ne kafin a hallara wajen wannan zaman.

Mai magana da yawun bakin shugaban majalisar dinkin Duniya, Antonio Guterres, Stephane Dujarric yace za a bi dokokin yaki da COVID-19 a wajen taron.

A shekarar da ta gabata, ba a iya hadu wa ido na ganin ido ba saboda annobar cutar COVID-19.

Kara karanta wannan

Buhari yace yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya yana da matukar wahala

NAN tace za a fara taron wannan shekara ne a ranar 14 ga watan Satumba, 2021, inda za a kaddamar da sabon shugaban zauren majalisar, Abdulla Shahid.

Yaki da miyagun kwayoyi

A makon nan ne aka samu labari cewa sojoji sun yi ram wani tsohon jami’in sojan da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi daga jihar Ondo zuwa jihohin Arewa.

Wasu tsofaffin mutane ‘Yan shekara 50 da 60 ne suka fada hannun sojoji da laifin dakon kwayoyi. Sojojin sun damka su hannun jami'an NDLEA domin ayi bincike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel