Asirin Wata Ma’aikaciyar Jinya Mai Amfani da Takardun Bogi Ya Tonu Bayan Ta Yi Watanni 3 Tana Amsar Albashi

Asirin Wata Ma’aikaciyar Jinya Mai Amfani da Takardun Bogi Ya Tonu Bayan Ta Yi Watanni 3 Tana Amsar Albashi

  • Hukumar lafiya ta jihar Legas ta damki wata Olafunke Adegbenro, ma’aikaciyar jinya a babban asibitin Isolo
  • Ana zargin ta da kwashe watanni 3 tana aiki kuma tana amsar albashi daga gwamnatin jihar Legas da takardun makaranta na bogi
  • An gano ta ne yayin wani taro na tantance ma’aikata da kungiyar ma’aikatan jinya da anguwar zoma ta jihar Legas ta gudanar a asibitin

Jihar Legas - Hukumar lafiya ta jihar Legas ta kama wata Olufunke Adegbenro wacce babban asibitin Isolo na jihar Legas ya dauka aiki tun watan Yulin 2021, bisa amfani da takardun makaranta na bogi.

Punch Metro ta bayyana yadda jami’an kungiyar ma’aikatan jinya da unguwar zoma ta kama Adegbenro a wani taro na tantance ma’aikata da su ka yi bayan ta kwashe watanni 3 tana amsar albashi daga wurin gwamnatin jihar.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Jam'iyyar APC ta fatattaki tsohon gwamna da wasu mambobi 40

Asirin Wata Ma’aikaciyar Jinya Mai Amfani da Takardun Bogi Ya Tonu Bayan Ta Yi Watanni 3 Tana Amsar Albashi
Ma’aikaciyar Jinya Mai Amfani da Takardun Bogi Da Aka Kama a Legas. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Duk takardun makaranta na bogi ne

Wakilin Punch Metro ya tattaro bayanai akan yadda Adegbenro ta yi takardar digiri a karatun jinya ta jami’ar fasahar Ladoke Akintola ta bogi, takardar shaidar bautar kasa, takardar rijistar zama cikakkiyar ma’aikaciyar jinya daga kungiyar ma’aikatan jinya da unguwar zoma da kuma lasisin yin aikin jinya duk na bogi.

Shugaban NANNM na jihar Legas, Olurotimi Awojide ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce yayin da ake tantance ma’aikatan asibitin aka gano ha’incin.

Kamar yadda ya ce:

“Kusan makwanni 2 kenan da suka gabata, muka fara tantace ma’aikata a asibitocin mu kuma babban dalilin mu na tantancewar shine mu gano wadanda basu sabanta lasisin su ba, kawai sai muka ga nata lasisin ba irin namu bane.
“An yi saurin janyo hankalin mu, a matsayi na na shugaban kungiyar, aka mika min lasisin don in duba shi kuma na tabbatar da cewa na bogi ne.

Kara karanta wannan

Macizai sun addabi jami'ar Katsina, ma'aikata sun shiga atisayen korar macizai

“Na same ta don na yi mata wasu tambayoyi kuma na amshi sauran takardun ta. Mun gayyaci ‘yan sanda dama wadanda suka kama ta suka nufi ofishin su. Ba su musa ko zargi daya da aka yi mata ba; ta tabbatar da cewa duk takardun makarantar ta na bogi ne kuma akwai wanda ya hada mata su a Ibadan.”

Manema labarai daga Punch Metro sun tabbatar da yadda lamarin ya faru a ofishin ‘yan sanda na Lions Building.

Shugaban ma’aikatan jinya na jihar bai furta komai ba akan lamarin

Shugaban ma’aikatan jinya na hukumar lafiya ta jihar Legas, Olaide Animashaun ya tabbatar da kama matar amma bai furta komai ba dangane da lamarin.

Sakataren lafiya na jihar Legas, Ademuyiwa Eniayewun, ya ce ba zai iya cewa komai ba dangane da lamarin ta waya, inda ya ce sai dai wakilin The Punch ya je har ofishin sa don tattaunawa.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta shawo kan Malaman asibitin da ke shirin bin kwararrun Likitoci zuwa yajin aiki

Jami’in hulda da jama’an rundunar ‘yan sandan jihar Legas, Adekunle Ajisebutu, ya ce zai yi bincike akan kama matar da aka yi kuma zai tuntubi Punch. Har yanzu ba a ji komai ba daga wurin sa.

'Yan sanda sun damke ma'aikacin banki da ya kwashewa kwastoma N10m daga asusunsa

A wani labarin daban, Hukumar ‘yan sandan jihar Oyo sun kama wani Adeyemi Tosin, mai shekaru 36, wanda ma’aikacin banki ne bisa zarginsa da kwasar naira miliyan 10 daga asusun wani abokin huldar bankin, Oladele Adida Quadri.

Kakakin hukumar, DSP Adewale Osifeso, ya bayyana hakan a wata takarda a ranar Talata, 17 ga watan Augusta, inda yace Tosin ya saci kudin Quadri, mai shekaru 78 ne da sunan zai taimake shi a reshen bankin na Ibadan bisa matsalar da ya samu wurin cirar kudi a ranar 12 zuwa ranar 13 ga watan Augusta.

Binciken ‘yan sandan ya haifi da mai ido sakamakon umarnin kwamishinan ‘yansandan jihar, Ngozi Onadeko, wacce tasa a yi bincike na musamman.

Asali: Legit.ng

Online view pixel