Gwamnati ta shawo kan Malaman asibitin da ke shirin bin kwararrun Likitoci zuwa yajin aiki
- Ministan kwadago da samar da aiki ya zauna da kungiyar JOHESU ta malaman asibiti
- Chris Ngige yace an ci ma matsaya kan albashi, alawus da shekarun ritayan ma’aikata
- Ngige ya bayyana cewa nan gaba ne ake sa ran a sa hannu a yarjejeniyar da aka cin ma
Abuja - Gwamnatin tarayya tace ta cin ma yarjejeniya da kungiyar hadakar ma’aikatan asibiti watau JOEHU da kungiyar majalisar ma’aikatan lafiya.
Jaridar The Cable ta rahoto Ministan kwadago da samar da aikin yi, Sanata Chris Ngige, yana wannan bayani a ranar Talata, 7 ga watan Satumba, 2021.
Chris Ngige ya yi magana da manema labarai a karshen zaman sa’o’i biyar da ya yi da kungiyoyin.
Sanata Chris Ngige yace an tsaida magana da shugabannin ma’aikatan lafiyan kasar, kuma za a sa hannu a takardar yarjejeniya ta MOU a mako mai zuwa.
Rahoton yace an cin ma matsaya game da sabanin da ake samu tsakanin ma’aikatan da gwamnati.
Kungiyar ta JOHESU ta bukaci a kara shekarun ritayar ma’aikatan lafiya daga 60 zuwa 65, sannan a biya su bashin kudin da suke bi, a kuma kara masu alawus.
Har ila yau, Ministan kwadagon yace za a kara kaurin tsarin albashin CONHESS kamar yadda aka yi wa tsarin albashin CONMESS na abokan aikinsu likitoci.
A cewar Ministan, gwamnati za ta zauna da kungiyar likitoci, kuma ba ta kokarin hana kowa alawus dinsa. A ranar Alhamis JOHESU za su sake yin zama.
Za a biya alawus - Ministan kwadago
“Mun nuna masu halin tattalin arzikin da mu ke ciki, sun kuma yi alkawari za su zauna da ‘ya ‘yansu, sannan su dawo gare mu.”
Sabon ministan wuta ga 'yan Najeriya: Kada ku yi tsammanin za a samar da wutan lantarki kamar sihiri
“A gefe guda kuma, gwamnatin tarayya za ta yi zama da kungiyar NMA a kan batun alawus dinsu. Tuni gwamnatin tarayya ta ware masu N37.5bn.”
PM News tace a farkon watan Satumba, kungiyar JOHESU ta bada wa’adin kwanaki 15, inda tace idan har ba a biya mata bukatunta ba, za ta tafi yajin-aiki.
A makon nan gwamnatin tarayya ta kafa kwamitin da zai bunkasa kiwon lafiya. Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo zai jagoranci wannan kwamiti.
Gwamnan Delta, Ministan lafiya, Farfesa N. Sambo, Dr. Sani Aliyu, da Dr. Mairo Mandara, suna cikin wadanda za su bada gudumuwa a farfado da kiwon lafiya
Asali: Legit.ng