'Dan mai gida ya yi wa ɗan hanya duka har sai da ya ce ga garinku

'Dan mai gida ya yi wa ɗan hanya duka har sai da ya ce ga garinku

  • Wani dan mai gida ya halaka wani da ke haya a gidan mahaifinsa a garin Oke Ijebu a Akure ta jihar Ondo
  • Mai gidan ya samu sabani da dan hayan ne hakan yasa ya kira dansa a waya domin ya zo ya shiga masa fada
  • Da isowar dan kawai sai ya dauki katako ya buga wa dan hayan a kansa hakan ya yi sanadin rasuwarsa

Jihar Ondo - 'Yan sanda a jihar Ondo sun kama wani dan wani mai gidan haya mai suna Sam Omojola bisa halaka mai haya a gidan mahaifinsa, Daily Trust ta ruwaito.

A cewar rahoton na Daily Trust, Omojola ya rafkawa marigayin katako ne a kansa yayin fada tsakanin marigayin da mahaifinsa.

Kara karanta wannan

Adamawa: Jarumin mai shago ya ragargaji ‘yan daba 2 da su ka yi kokarin fasa masa shago

'Dan mai gida ya yi wa ɗan hanya duka har sai da ya ce ga garinku
Taswirar Jihar Ondo. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abin bakin cikin ya faru ne a unguwar Oke Ijebu da ke Akure, babban birnin jihar ta Ondo.

Yaya lamarin ya faru?

An tattaro cewa rikici ya barke ne a lokacin da mai gidan ya samu rashin jituwa tsakaninsa da marigayin da ke haya a gidansa saboda batun biyan kudin haya.

Mai gidan, wanda aka ce ya zargi dan hayan da zaginsa, ya daga wayarsa ya kira dansa.

A cewar majiyar yan sanda, a lokacin da dan sa ya iso, a maimakon ya yi tambaya ya ji abin da ya faru tsakanin mahaifinsa da marigayin, kawai sai ya dauki katako ya buga wa dan hayan a kansa.

Daga nan ne fa ya fadi kasa, jini na zuba kuma nan take makwabta suka garzaya da shi asibiti inda aka kwantar da shi amma ya ce ga garin ku bayan kwanaki biyu.

Kara karanta wannan

Plateau: Sojojin OPSH sun yi wa direban tasi dukan fitar rai a Jos

Bayan samun rasuwar marigayin, 'yan uwansa da abokansa sun taru sun tafi gidan mai gidan hayan da nufin su bankawa gidan wuta.

'Yan sanda sun shiga lamarin

Amma isowar jami'an yan sanda daga caji ofis na Ijabo ya hana su kona gidan.

'Yan sandan sun kama wanda ake zargi da sanadin kisar sun fara gudanar da bincike.

Wani mutum ya gamu da ajalinsa yayin da ya shiga maƙabartar musulmi cikin dare don haƙo gawa

A wani kabarin daban, wani mutum da ba a gano ko wanene ba ya mutu yayin da ya ke yunkurin hako gawa a makabarta da ke Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, Premium Times ta ruwaito.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a makabartar musulmi da ke Iberekodo, karamar hukumar Abeokuta ta Arewa na jihar Ogun.

Abimbola Oyeyemi, mai magana da yawun yan sandan jihar Ogun, ya tabbatarwa Premium Times afkuwar lamarin a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Buhari yace yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya yana da matukar wahala

Asali: Legit.ng

Online view pixel