Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan Ya Magantu Kan Raɗe-Raɗin Shigarsa Jam’iyyar APC

Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan Ya Magantu Kan Raɗe-Raɗin Shigarsa Jam’iyyar APC

  • Dr Goodluck Ebele Jonathan, tsohon shugaban Nigeria ya karyata jita-jitar cewa ya koma jam'iyyar APC
  • A ranar Laraba ne wata rahoto ta rika yawo a dandalin sada zumunta da ke cewa Jonathan ya koma APC don ya yi takara a 2023
  • Ikechukwu Eze, mai magana da yawun Jonathan ya ce rahoton ba gaskiya bane ya kara da cewa mai gidansa ya dukufa wurin yin wasu ayyukan

Tsohon shugaban Nigeria, Goodluck Ebele Jonathan ya musanta cewa ya koma jam'iyyar All Progressives Congress, APC, mai mulki a kasar, SaharaReporters ta ruwaito.

A ranar Laraba, wani rahoto ya bazu a dandalin sada zumunta cewa tsohon shugaban kasar ya nuna sha'awar yana son ya fice daga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP.

Goodluck Jonathan Ya Magantu Kan Rade-Radin Shigarsa Jam’iyyar APC
Tsohon Shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan. Hoto: SaharaReporters
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Jam'iyyar APC ta fatattaki tsohon gwamna da wasu mambobi 40

Rahoton ya kara wa jita-jitar cewa tsohon shugaban kasar yana da shirin sake fitowa takarar shugaban kasa a 2023 karfi.

Mai magana da yawun Jonathan ya karyata rahoton

Amma a martaninsa, Ikechukwu Eze, mai magana da yawun Jonathan ya ce rahoton labarin kanzon kurege ne.

Eze ya ce:

"Rahoton ba gaskiya bane. Idan ya sauya sheka zuwa wata jam'iyyar. Za a sanar ta kafar da ta dace."

Ya jadada cewa mai gidansa bai nuna alama ko niyyar komawa jam'iyyar APC mai mulki ba.

Ya kara da cewa:

"Mutumin nan fa yanzu akwai wasu abubuwa masu muhimmanci da suka shige masa gaba."

2023: Ba mu buƙatar Atiku ya sake takara, Ya tafi Dubai ya manta da mu tunda ya sha kaye a 2019, Ƙungiyar PDP

A wani labarin daban, wata kungiya mai suna People’s Democratic Party (PDP) Action 2023, ta bukaci tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar kada ya sake takara a shekarar 2023 don ya yi watsi da jam'iyyar ya koma Dubai, UAE, tunda ya fadi zabe a 2019, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Coci ya ruguje kan masu bauta ana cikin ibada a Taraba, ya hallaka mutane biyu

Atiku, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2019, bai riga ya bayyana niyarsa na son sake takara ba a 2023, amma, dansa, Adamu Atiku Abubakar, ya tabbatar cewa zai sake takara.

Amma a martaninsa, Atikun ya ce ba watsi da jam'iyyar ta PDP ya yi ba, ya tafi yin karatun digiri na biyu ne a kasar waje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel