Dagaci da mazauna kauye sun tsere bindi-zage bayan wani abin tsafi ya yi ajalin mutane 7 a Adamawa

Dagaci da mazauna kauye sun tsere bindi-zage bayan wani abin tsafi ya yi ajalin mutane 7 a Adamawa

  • Shugaba da mazauna kauyen Dasin Bwate da ke karamar hukumar Fufore a jihar Adamawa sun yi hijira
  • Ganin wani rikitaccen tsafi mai ban tsoro wanda ya yi ajalin mutane 7 ne yasa suka kasa hakurin jiran daukin jami’an tsaro
  • Sai dai yanzu haka shugaban rundunar ‘yan sandan yankin, DSP Sulaiman Nguroje ya sa ayi bincike dangane da sarkakiyar

Jihar Adamawa - Daga Dagajin kauyen Dasun Bwate na karamar hukumar Fufore a jihar Adamawa har mazauna yankin sun tsere bayan wani lamari da aka fi zargin tsafi ne ya yi ajalin mutane 7 a kauyen.

Mazauna yankin sun kasa hakurin jiran jami’an tsaro su kawo taimako hakan ya sa suka yanke shawarar yin hijira don neman tsira.

Dagaci da mazauna kauye sun tsere bindi-zage bayan wani abin tsafi ya yi ajalin mutane 7 a Adamawa
Abin tsafi. Hoto: News Wire NGR
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan Boko Haram sun koma dajin Kaduna – DSS ta ankarar da sauran hukumomi

Sai dai shugaban rundunar ‘yan sandan yankin, DSP Sulaiman Nguroje ya tabbatar da aukuwar lamarin kamar yadda News Wire NGR ta tabbatar.

A cewar sa:

“Mutane 7 ne suka halaka a Kauyen Dasin Bwate da ke karamar hukumar Fufore dalilin wani lamari da ake zargin tsafi ne.
“An tura rundunar ‘yan sanda don su je kauyen su binciko gaskiyar al’amarin,” kamar yadda News Wire NGR ta ruwaito Nguroje ya ce.

Rundunar ‘yan sanda ta tsinci gawawwaki guda 7 duk a wani gida da ke cikin kauyen

A cewar Nguroje ‘yan sanda sun tsinci gawawwaki har 7 a wani gida sai dai duk ‘yan kauyen sun riga sun yi hijira shiyasa har yanzu ba a riga an kama kowa ba a cewar sa.

Ana cigiyar inda ‘yan kauyen suke don su bayar da bayanai

Ya bukaci makwabta da su bai wa ‘yan sanda hadin-kai da bayanai wadanda za su sa a gano gaskiyar inda mazauna kauyen suke don jin abinda ya faru.

Kara karanta wannan

Gwamnan Zamfara Matawalle Zai Farfaɗo Da Rundunar ‘Yan Sa Kai’ Don Kawar Da Ta’addanci a Jihar

“Muna kira ga makwabtan kauyen da su taimaka wa ‘yan sanda da bayanai masu amfani akan inda mazauna Dasin Bwate suke,” kamar yadda Nguroje ya ce.

Adamawa: Jarumin mai shago ya ragargaji ‘yan daba 2 da su ka yi kokarin fasa masa shago

A wani rahoton, kun ji wani mai shago, Mohammed Hamman Adama, ya nuna gwarzontakarsa bayan ya yi dambe da wasu yaran Shila yayin da su ka yi kokarin balle masa shagon sa da ke Sangere Bode a karamar hukumar Yola ta kudu a jihar Adamawa.

LIB ta ruwaito yadda aka tattaro bayanai akan wadanda ake zargin, Umar Sa’ad, mai shekaru 18 da Mohammed Idris, mai shekaru 20 suka lallaba shagon sa da misalin karfe 2:00 na daren 2 ga watan Satumban 2021 da addunan su, gudumomi, sanduna da sauran miyagun makamai.

Bayan isar su shagon har sun fara balle kofar don su samu nasarar yasar shagon. Su na kici-kicin balle kofa mai shagon ya ji kara ya fita cikin sauri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel