Jerin jihohi 5 da za su amfana yayin da FG ta amince da ayyukan titin N38bn
- A ranar Laraba, 15 ga watan Satumba, Gwamnatin Tarayya ta amince da Naira biliyan 38.4 don kammala ayyukan hanyoyi a jihohi biyar
- Jihohin da za su ci moriyar wannan aiki sun hada da Benue, Bayelsa, Anambra, Imo da kuma Nasarawa
- Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola ne ya bayyana hakan bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya wanda ya gudana a fadar shugaban kasa, Abuja
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya a ranar Laraba, 15 ga Satumba ta amince da Naira biliyan 38.4 don kammala ayyukan hanyoyi a jihohi biyar.
Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola ne ya bayyana hakan bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC), jaridar The Cable ta ruwaito.
Jihohin da su amfana sun hada da:
1. Benue
2. Bayelsa
3. Anambra
4. Imo
5. Nasarawa
A cewar Fashola, dukkan ayyukan an gaje su ne daga gwamnatocin baya.
Daya daga cikin kwangilolin shine hanyar Onitsha-Owerri ta Okija-Ihembosi-For Ugbor zuwa Ezinifite a karamar hukumar Nnewi ta kudu na Anambra.
Wani kuma shi ne raba kilomita 20 na hanyar Yenagoa zuwa Kolo, Otuoke da Bayelsa Palm a jihar Bayelsa.
Ministan ya ce kwangila ta uku ita ce ta kammala hanyar da ta hada jihohin Nasarawa da Binuwai, Premium Times ta kuma ruwaito.
FG ta magantu kan lokacin da za ta sakar wa 'yan Nigeria Twitter su cigaba da morewa
A wani labari na daban, mun ji cewa gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce kwanan nan za ta dawo da kafar sada zumuntar zamani ta Twitter domin 'yan kasar su cigaba da morewa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito The Cable ta ruwaito.
Ministan labarai, Lai Mohammed ya bayyana hakan yayin amsa tambayoyin manema labaran cikin gidan gwamnati bayan kammala wani taro da majalisar zartarwa ta tarayya a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Mohammed ya ki sanar da tsayayyen lokacin da za a dage dokar, inda yace ga dukkan alamu tattaunawar gwamnati da Twitter akwai fahimta sannan an kusa kai matsaya.
Asali: Legit.ng