FG ta magantu kan lokacin da za ta sakar wa 'yan Nigeria Twitter su cigaba da morewa

FG ta magantu kan lokacin da za ta sakar wa 'yan Nigeria Twitter su cigaba da morewa

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa kwanan nan za ta dage dokar dakatar da fitacciyar kafar sada zumuntar zamani ta Twitter
  • Ministan Labarai, Lai Mohammed ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da manema labaran cikin gidan gwamnati suka yi da shi
  • Bai sanar da tsayayyen lokaci ba, sai dai ya ce da alamu tattaunawar da gwamnati tayi da Twitter an kusa samun matsaya

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce kwanan nan za ta dawo da kafar sada zumuntar zamani ta Twitter domin 'yan kasar su cigaba da morewa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito

The Cable ta ruwaito, Ministan labarai, Lai Mohammed ya bayyana hakan yayin amsa tambayoyin manema labaran cikin gidan gwamnati bayan kammala wani taro da majalisar zartarwa ta tarayya a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda da 'yan bindiga sun mamaye murabba'in mita 1,129 na gandun dajin Najeriya

FG ta magantu kan lokacin da za ta sakar wa 'yan Nigeria Twitter su cigaba da morewa
Ministan Sadarwar Nigeria, Lai Mohammed. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Mohammed ya ki sanar da tsayayyen lokacin da za a dage dokar, inda yace ga dukkan alamu tattaunawar gwamnati da Twitter akwai fahimta sannan an kusa kai matsaya.

Lai Mohammed bai bayar da tsayayyen lokacin dage dokar ba

An tambaye shi tsayayyen lokacin da za a dage dokar kamar yadda ya sanar a ranar 11 ga watan Augusta, ya ce kwanan nan dai za a dage dokar:

“Ina ga ko kwana 2 da suka gabata Twitter ta ce suna tattaunawa kuma da alamun nasara da fahimtar juna tsakanin su da gwamnatin tarayya,” kamar yadda Daily Trust ta ruwaito Mohammed ya ce.
“Batun zuwa wanne lokaci za a dage dokar, Ina so in tabbatar muku da cewa ba za a kai dadewar da aka yi a baya ba, tun daga lokacin da aka dakatar da kafar zuwa yanzu, nan kusa za a kawo matsaya."

Kara karanta wannan

Kebbi: Iyayen daliban FGC Yauri sun cire rai gwamnati za ta karbo musu 'ya'yansu

“Wuraren kwana 100 kenan da dakatar da wannan kafar, yanzu kuwa muna batun nan kusa za a dage dokar don haka daga yanzu zuwa ko wanne lokaci a dawo da Twitter.
“Muna kokarin ganin mun gyara abubuwan da suke faruwa, amma mun san yadda ‘yan Najeriya da dama suka kosa a dawo da kafar kuma yanzu haka kokarin da ake yi kenan.
“Sannan ita kanta Twitter ta ce an samu canji daga duk bangarorin (bangaren ta da gwamnatin tarayya). Kuma akwai ganin girma sosai tsakanin su. Mun gode kwarai."

An kara tambayar sa tsayayyen lokacin da za a dage dokar, sai Mohammed ya ce:

“Gaskiya mun yi nisa, kuma ba zan iya cewa ga tsayayyen lokaci ba. Amma dai kwannan nan, kawai ku yarda da magana ta."

Gwamnatin tarayya ta ce Twitter ta samar wa da mutane damar kawo barazanar tashin hankali a Najeriya.

Ana zargin Jack Dorsey, mai kamfanin Twitter, da taimakon mutane da kudi wurin yin zanga-zangar EndSARS sannan kafar ta bai wa shugaban IPOB, Nnamdi Kanu damar amfani da kafar wurin kira ga halaka ‘yan sanda.

Kara karanta wannan

Binciko Gaskiya: Da gaske ne DSS sun kama telan Buhari da ya yi masa dinkin Imo?

Don haka gwamnati ta gindaya dokoki wanda wajibi ne Twitter ta bi. An samu rahotanni akan yadda Najeriya ta rasa dala miliyan 360 sakamakon dakatar da Twitter.

Asali: Legit.ng

Online view pixel