Babu wasikar jan kunne da 'yan bindiga suka aiko mana, FGC Sokoto

Babu wasikar jan kunne da 'yan bindiga suka aiko mana, FGC Sokoto

  • FGC Sokoto ta musanta labarin da ke yawo cewa hukumar makarantar ta rufe ta saboda matsalar tsaro
  • Shugaban hukumar makarantar, Ibrahim Uba ne ya bayyana hakan a wata takarda inda ya ce babu wani matsalar rashin tsaro
  • Kamar yadda ya bayyana, an rufe makarantar ne saboda sun kammala jarabawar canji aji kuma an zo karshen zangon karatu

Sokoto - Hukumar makarantar FGC Sokoto ta musanta labarin da ya yi ta yawo a kan ta rufe makarantar ne saboda matsalar tsaro.

Daily Trust ta ruwaito cewa, a wata takarda wacce shugaban hukumar makarantar, Ibrahim Uba ya sa hannu, ya ce babu batun wata barazana da aka yi wa makarantar.

Babu wasikar jan kunne da 'yan bindiga suka aiko mana, FGC Sokoto
Babu wasikar jan kunne da 'yan bindiga suka aiko mana, FGC Sokoto. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

“In fayyace muku bayani, a ranar Litinin, 13 ga watan Satumba, kungiyar daliban FGC Birnin Yauri 13 aka maido makarantar saboda wani mummunan lamari da ya auku a makarantar a wasu watannin da suka gabata.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan bindiga sun bindige shugaban cocin Anglika har lahira a Imo

“Ba mu yanke shawarar rufe makarantar ba sakamakon wata wasika da ‘yan bindiga suka tura wa hukumar shugabancin makarantar, sai dai labarin hakan ya janyo tashin hankali da damuwa a wurin dalibai da malaman makarantar.
“Sai dai hukumar makarantar ta yi kokarin kore tsoro daga zuciyoyin su inda ta ce babu wata takarda da ‘yan bindiga suka tura mata sannan babu wata matsalar rashin tsaro a makarantar,” kamar yadda takardar ta bayyana.

Takardar ta kara da cewa, hukumar makarantar ta nemi tallafin jami’an tsaro don a rufe makarantar don gudun ci gaba da tada wa dalibai hankali, don haka suka kammala jarabawar karshen zango suka rufe makarantar.

Ta kara da cewa makarantar ta tuntubi jami’an tsaro don kulawa da rayuka da dukiyoyin dalibai da malamai, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Daliban Zamfara 75 da aka sace sun samu 'yanci bayan kwanaki 11

“Duk da gaggawar rufe makarantar, yanzu haka akwai shirin komawar dalibai makaranta musamman wadanda yanzu haka suke zana jarabawar WAEC kuma suke son zama a makarantar.”

Daily Trust ta ruwaito yadda wasu mutane (ba malaman makarantar ba) su ke ta faman kiran iyaye suna cewa su zo su dauke yaransu daga makarantar, ‘yan bindiga sun turo wasika makarantar kuma za su kawo farmaki.

IGP ya nada sabuwar mai magana da yawun rundunar 'yan sandan FCT

A wani labari na daban, Sifeta janar na ‘yan sanda, Usman Baba ya amince da nadin DSP Josephine Adeh a matsayin jami’ar hulda da jama’an rundunar ‘yan sanda na babban birnin tarayya, Abuja.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, a wata takarda wacce ya saki a ranar Talata a Abuja, ya ce sabuwar jami’ar hulda da jama’ar za ta fara aiki ne take-yanke.

Adeh ta maye gurbin ASP Daniel Ndirpaya ne wanda yanzu aka yi wa karin girma zuwa kwamishinan ‘yan sanda na Abuja a ranar 31 ga watan Augusta.

Kara karanta wannan

NEDC ta fara gina makarantu ga talakawa a yankunan da Boko Haram ta addaba

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: