IGP ya nada sabuwar mai magana da yawun rundunar 'yan sandan FCT
- Sifeta janar na ‘yan sanda, Usman Baba, ya amince da nadin DSP Josephine Adeh a matsayin jami’ar hulda da jama’an rundunar ta Abuja
- Ya bayyana hakan a wata takarda ta ranar Talata a Abuja inda yace za ta fara aiki ne take yanke kuma ta maye gurbin ASP Daniel Ndirpaya
- Dama kamar yadda rahotanni suka tabbatar, kafin a nada ta a wannan matsayin, Adeh ce ta biyu a harkar sadarwa ta musamman bangaren hulda da jama’a
FCT, Abuja - Sifeta janar na ‘yan sanda, Usman Baba ya amince da nadin DSP Josephine Adeh a matsayin jami’ar hulda da jama’an rundunar ‘yan sanda na babban birnin tarayya, Abuja.
Daily Nigerian ta ruwaito cewa, a wata takarda wacce ya saki a ranar Talata a Abuja, ya ce sabuwar jami’ar hulda da jama’ar za ta fara aiki ne take-yanke.
Adeh ta maye gurbin ASP Daniel Ndirpaya ne wanda yanzu aka yi wa karin girma zuwa kwamishinan ‘yan sanda na Abuja a ranar 31 ga watan Augusta.
Kamar yadda takardar ta bayyana, a da Adeh ce ta biyu a harkokin sadarwa na bangaren hulda da jama’a kafin a yi mata wannan nadin.
An ce sabuwar PPRO ta taba rike mukamin mataimakiyar mai bayar da shawarar ‘yan sanda na Police Attache a New York a Amurka.
“Adeh daya ce daga cikin mambobin Nigerian Institute of Public Relations sannan memba ce ta International Association of Chiefs of Police.
“Ta yi karatun Advanced Detective Course a Police Staff College da ke Jos,” kamar yadda takardar ta bayyana.
Sannan takardar ta ce za a iya samun sabuwar PPRO din ta lambar waya 07038979348 ko kuma Public Complaint Bureau a 09022222352 ko kuma adireshin yanar gizo na fctpolice@gmail.com
Bayan 'yan fashin daji sun raba wasika, an tura karin 'yan sanda Sokoto
A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Sokoto ta tura jami'ai yankunan da ake zargin miyagun 'yan fashin daji za su kai farmaki a jihar.
Premium Times ta ruwaito yadda wasu 'yan bindiga a makon da ya gabata suka raba wasika a harshen hausa inda suka sanar da yankunan shirinsu na kai musu farmaki.
A wasikar, 'yan bindigan sun sanar da mazauna yankin cewa, za su iya gayyatar sojoji sama da dari domin ba su kariya amma sai sun kai farmakin.
Asali: Legit.ng