NDLEA sun yi nasarar dakile kilogram 24, 311 na Koken, Codeine da kwayoyi da za a shigo da su

NDLEA sun yi nasarar dakile kilogram 24, 311 na Koken, Codeine da kwayoyi da za a shigo da su

  • Jami’an hukumar NDLEA sun tare wasu kwayoyi da aka shigo da su ta Legas
  • Wani jami’in NDLEA Femi Babafemi yace an tare tulin Codeine da hodar iblis
  • An yi ram da wadannan kaya ne a tashohin Tincan da filin jirgin saman Ikeja

Lagos - Hukumar NDLEA mai yaki da masu safarar miyagun kwayoyi na kasa ta karbe kilogram na 24, 311 na hodar iblis da wasu kwayoyi a Legas.

Hukumar NDLEA ta bada wannan sanarwa a shafinta na Facebook a ranar Lahadi, 12 ga watan Satumba, 2021, a wasu tashoshin da ke garin Legas.

Rahoton ya bayyana cewa an tsare wadannan miyagun kwayoyi ne a babban filin tashin jirgin sama na Murtala Mohammed da tashar ruwar Tincan.

Kara karanta wannan

Da dumi dumi: Yan bindiga sun kashe tsohon sarkin da aka dakatar saboda ziyartar Buhari

Jaridar Reuben Abati ta rahoto cewa shugaban yada labarai da wayar da kan al’umma na NDLEA, Femi Babafemi ne ya fitar da jawabi na musamman.

Mista Femi Babafemi yace a ranar 3 ga watan Satumba jami’an NDLEA da ke bakin aiki a filin jirgin Murtala Mohammed suka tare da wasu tulin kaya.

An gano cewa kayan na dauke da kilogram 10.35 na kwayar heroine da kuma kilogram 25.2 na ganyen tabar wiwi da aka yi safara daga Afrika ta Kudu.

NDLEA
Miyagun kwayoyi Hoto: @ndlea01
Asali: Facebook
“A wasu samame a jere da aka kai a yankunan Legas a tsakanin 4 ga watan Satumba zuwwa 6 ga watan satumban, mun kama mutane hudu da ake zargi da laifi.
“An cafke Misis Bello Kafayat Ayo a layin Shino da ke cikin unguwar Palmgroove a jihar Legas.”

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun far ma matafiya, sun yi garkuwa da mutum 5 a Ondo

“A tashar ruwan Tincan da ke Apapa, malaman migayun kwayoyi sun tare kontena mai taku 40 wanda ya dauko kilogram 22. 590 na ruwan Codeine.”

Ba yau aka fara ba

NDLEA ta yi wannan babban kamu ne jim kadan bayan ta kama wani mutumi yana kokarin shigo da kwayoyin Amphetamine a babban tashar ruwa na Apapa.

Daga cikin wadanda aka kama a garuruwa da dama, jaridar tace wasu sun amsa laifinsu tuni.

A makon da ya gabata aka ji labarin wani magidanci a Delta da ya kashe Uwargidarsa da mugun duka saboda ta hana shi abincin dare bayan ya kwankwadi giya.

Duk da Mai dakinsa ta na shirin haihuwa ko yau ko gobe, wannan mutumi yayi mata duka har lahira. Marigayiyar ita ce e uwar ‘ya ‘yansa hudu da suka samu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng