Da Dumi-Dumi: An Tsige Shugaban Masu Rinjaye Na Majalisar Dokokin Jihar Kaduna

Da Dumi-Dumi: An Tsige Shugaban Masu Rinjaye Na Majalisar Dokokin Jihar Kaduna

  • 'Yan majalisar dokokin jihar Kaduna sun tsige Mohammed Inuwa, shugaban masu rinjaye na majalisar
  • An tsige Inuwa ne a ranar Laraba bayan da 'yan majalisa na APC 17 suka rattaba hannu kan takardan tsige shi
  • Tanimu Musa, Shugaban kwamitin sadarwa na majalisar ya ce nan gaba za su sanar da sabon shugaban masu rinjaye

Kaduna - Majalisar dokokin jihar Kaduna ta tsige Mohammed Inuwa, shugaban masu rinjaye na majalisar, The Cable ta ruwaito.

An tsige Inuwa, mai wakiltar mazabar Doka/Gabasawa ne a ranar Laraba kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Da Dumi-Dumi: An Tsige Shugaban Masu Rinjaye Na Majalisar Dokokin Jihar Kaduna
Majalisar Dokokin Jihar Kaduna. Hoto: The Leadership
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An cimma matsayar hakan ne bayan da mambobin majalisar suka jefa masa kuri'an rashin amincewa da jagorancinsa.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Hotuna sun bayyana yayin da Buhari ya rantsar da sabbin kwamishinonin INEC

'Yan majalisar APC 17 sun ratabba hannu kan wasikar tsige shi

A cewar kamfanin dillancin labarai na NAN, mambobin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) su 17 ne suka rattaba hannu kan wasikar tsige shi.

Da ya ke magana da manema labarai jim kadan bayan zaman majalisar, Tanimu Musa, Shugaban kwamitin sadarwa na majalisar, ya ce kan yan majalisar ya hadu wurin kuri'un rashin amincewar.

Ya ce:

"Don haka, Mabo zai kasance tsigagen shugaba har zuwa lokacin da za a sanar da sabon shugaban masu rinjaye."

An dakatar da mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar Nasarawa

A ranar Talata, Majalisar jihar Nasarawa ta dakatar da Luka Zhekaba, mataimakin shugaban marasa rinjaye, kan zarginsa da hannu wurin daukan malaman makaranta 38 na bogi aiki a jihar.

An dakatar da Zhekaba ne bayan an tattauna kan rahoton dauka malamai 366 inda ka gano malaman bogi 38 suna karbar albashi.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan bindiga sun bindige shugaban cocin Anglika har lahira a Imo

An kafa kwamiti ta wucin gadi ne don bincike kan hannunsa a cikin dakan ma'aikatan na bogi.

Tsaro: Gwamnatin Kaduna ta hana yawon gararamba da ayyukan sare itatuwa a dazukan jihar

A wani labarin daban, Gwamnatin Jihar Kana ta haramta yawon 'gararamba' a gari da shiga manyan dazuka a jihar domin yin ayyuka, The Cable ta ruwaito.

Jihar ta kuma hana sare itatuwa domin yin aikin kafinta, girki da gawayi a kananan hukumomi bakwai a jihar saboda karuwar matsalar rashin tsaro.

Kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro na jihar Samuel Aruwan ne ya bada sanarwar a ranar Talata kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel