Tsaro: Gwamnatin Kaduna ta hana yawon gararamba da ayyukan sare itatuwa a dazukan jihar

Tsaro: Gwamnatin Kaduna ta hana yawon gararamba da ayyukan sare itatuwa a dazukan jihar

  • Gwamnatin Jihar Kaduna ta hana yawon gararamba da shiga dazuka domin sare itatuwa a kananan hukumomi bakwai
  • Kananan hukumomin da abin ya shafa sun da Birnin Gwari, Igabi, Chikun, Giwa, Kachia, Kauru da Kajuru
  • Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce an dauki matakin ne domin inganta tsaro kuma ta duk wanda aka kama yana saba dokar zai fuskanci doka

Gwamnatin Jihar Kana ta haramta yawon 'gararamba' a gari da shiga manyan dazuka a jihar domin yin ayyuka, The Cable ta ruwaito.

Jihar ta kuma hana sare itatuwa domin yin aikin kafinta, girki da gawayi a kananan hukumomi bakwai a jihar saboda karuwar matsalar rashin tsaro.

Tsaro: Gwamnatin Kaduna ta hana yawon gararamba da ayyukan sare itatuwa a dazukan jihar
Taswirar Jihar Kaduna. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro na jihar Samuel Aruwan ne ya bada sanarwar a ranar Talata kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Aruwan ya ce an bada sanarwar ne bayan gwamnatin ta gana da kungiyar masu sayar da itatuwa, katako, da gawayi a jihar.

Kananan hukumonin da dokar ta shafa?

Ya lissafa kananan hukumomin da abin ya shafa kamar haka, Birnin Gwari, Igabi, Chikun, Giwa, Kachia, Kauru da Kajuru.

Sanarwar ta ce:

"Domin inganta tsaro ga kowa a jihar, bayan samun shawarwari daga hukumomin tsaro, gwamnatin jihar Kaduna ta dakatar da sare bishiya don katako, girki, gawayi da wasu harkokin cinikayya a kananan hukumomin Birnin Gwari, Igabi, Chikun, Giwa, Kachia, Kauru da Kajuru nan take.
"An kuma hana dukkan yawon gararamba da ayyuka a manyan dazukan da suke kananan hukumomi bakwai da aka lissafa, dokar ta fara aiki nan take."

Aruwan ya shawarci mazauna jihar da su guji aikata abubuwan da aka hana yana mai cewa hukumomin tsaro za su tabbatar an bi dokar.

A watannin baya-bayan nan an ta sace mutane da kai hare-hare a jihar Kaduna.

Kashe-kashen Plateau: An yi ram da mutum 10, Lalong ya shiga taron tsaro na gaggawa

A wani labarin daban, an kama mutane 10 da suke da alaka da kai sabon hari kauyen Yelwa Zangam na Jos ta arewa da ke jihar Filato, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Gwamna Simon Lalong ya kwatanta harin a matsayin rashin imani, sannan ya shirya taro na gaggawa don tattaunawa da kuma neman hanyar kawo garanbawul ga kashe-kashen da aka maimaita a jiharsa.

A wata takarda wacce darektan watsa labarai ya saki, Makut Mechan, ya ce gwamnan ya umarci jami’an tsaro su binciko duk wadanda suke da hannu a lamarin da masu daukar nauyinsu don a hukunta su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel