Hotunan ‘Pre-wedding’ din Jaruma Adamar Kamaye da wani Matashi suna yawo

Hotunan ‘Pre-wedding’ din Jaruma Adamar Kamaye da wani Matashi suna yawo

  • Hotunan auren Zahara’u Saleh da Mudassir Isyaku Dutsinma suna yawo
  • ‘Yar wasa Adamar Kamaye tayi karin haske game da wadannan hotunan
  • Jarumar tace ba aure ta yi ba, an dauki hotunan ne a wani fim da zai fito

Kano - Jaridar Katsina Post ta rahoto cewa ana jita-jitar shahararriyar ‘yar wasan kwaikwayo Zahara’u Saleh (Adamar Kemaye) ta auri wani matashi.

Zahara’u Saleh wanda ake kira Adamar Kamaye saboda suna da ta yi a shirin Dadinkowa ta amarce da wani mutumin garin Dutsinma a jihar Katsina.

Ba aure na yi ba

Domin a tabbatar da gaskiyar wannan rahoton, mujallar Fim ta tuntubi Hajiya Zahara’u Saleh, inda ta shaida cewa ba aure ta yi ba, hotunan wani fim ne.

Kara karanta wannan

Yadda rikicin Zamfara ya dauko asali shekaru 150 da suka wuce tun kafin zuwan Bature

Tauraruwar tace an dauki wadannan hotuna ne a wani fim da take shiryawa mai suna ‘Matan Yaro’. ‘Yar wasar tace tana sa rai wata rana ta samu mijin aure.

“Wannan hotunan na biki ne wanda amarya da ango su ke ɗauka kafin biki, watau ‘prewedding’, amma kuma a cikin fim.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Wallahi ba aure na yi ba. Wannan hotunan fim ɗi na ne wanda zai fito kwanan nan mai suna ‘Matar Yaro’.
Jaruma Adamar Kamaye
Mudassir Isyaku Dutsinma da Adama Dadinkowa
Asali: Instagram

A cewar jarumar, wannan sabon fim na ta zai kasance mai dogon zango kamar shirin Dadinkowa da ya kara fito da ita, wanda aka dauki lokaci ana haska wa.

“Fim ɗin zai kasance mai dogon zango kuma ni ce wacce na ɗauki nauyin shirya abu na da kai na.”

Da take magana da mujallar, Adama ta nuna farin ciki da yadda wannan fim yake samun karbu wa tun yanzu, tace ba da dade wa ba fim din zai shigo kasuwa.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya bayyana wanda ya dace da mulki, ya cire Osinbajo, Tinubu a lissafin 2023

Aliyu Tage ya rasu

Dazu aka ji Allah ya yi wa fitaccen jarumin Kannywood, kuma mai daukar hoto a masana’antar shirya fina-finan Hausa, Aliyu Ahmad Tage rasuwa.

Rahoton ya bayyana cewa Ahmad Tage ya rassu ne a ranar Litinin, 13 ga watan Satumba a jihar Kano bayan ya yi fama da yar gajeruwar rashin lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel