MIST: Gwamnatin Buhari ta amince wa sabuwar Jami’ar da aka kafa a Katsina ta fara aiki
- Gwamnatin Tarayya ta ba makarantar MIST da ke Katsina damar fara karatu
- Ma’aikatar harkokin jirgin sama tace daga yanzu MIST za ta iya daukar dalibai
- An samu sahun farko na daliban da suka shiga MIST, suna yin karatun difloma
Katsina - Gwamnatin tarayya ta ba hukumar NiMet damar fara karatu a makarantar Meteorological Institute of Science and Technology (MIST).
Jaridar Leadership tace mai magana da yawun bakin hukumar NiMet, Muntari Ibrahim Yusuf, ya bada wannan sanarwa, yace takarda ta fito daga ofishin Minista.
A wata wasika da Ma’aikatar harkokin jiragen sama ta aiko wa makarantar MIST a ranar 9 ga watan Satumba, 2021, ta amince da rokonta na fara yin karatu.
MIST za ta iya fara aiki
Mataimakiyar Darektar sashen horaswa da walwalar ma’aikata ta ma’aikatar, Rabi Abubakar ta sa hannu a wannan takarda a madadin Minista, Sanata Hadi Sirika.
“Ina maida martani ga takardarku mai lamba NiMet/DG/FMA/HMA/M/Vol.1/30 da aka aiko a ranar 24 ga watan Agusa, 2021, a kan wannan batu.”
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Kuna neman Mai girma Minista ya bada dama a fara karatu a sabuwar makarantar kimiyya da fasahar yanayi ta MIST, Katsina, kamar yadda kuka bukata.”
An rahoto Muntari Ibrahim Yusuf yana cewa makarantar ta fara gudanar da darusa ga masu yin difloma a fannin fahimtar yanayi da nazarin sauyin yanayi.
“An dauki dalibai ne ta hanyar tsarin JAMB. Hukumar NBTE ta amince a fara yin difloma a wadannan fannoni, an samu rukunin dalibai 30 a kowane aji.”
A Mayun 2019 Mai girma Ministan jiragen sama, Hadi Sirika ya kaddamar da makarantar MIST da nufin a bunkasa ilmin fahimtar yanayi da sauyin yanayi.
Yusuf yace MIST ta samu karin ma’aikata bayan samun wannan dama, yanzu akwai malamai masu Ph.D takwas, ciki akwai Farfesoshi biyar, da masu digirgir.
An kashe mutane 12 a Kaduna
Gwamnatin jihar Kaduna ta bakin kwamishinan harkoki da tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, ta tabbatar da mutuwar mutum 12 a harin da aka kai a Zangon Kataf.
Yayin da mutane 12 suka bakunci barzahu, akwai mutane biyu da suke jinya a gadon asibiti.
Asali: Legit.ng