Karin bayani: Jami'an tsaro sun kamo fursunoni 108 da suka tsere daga gidan yarin Kogi

Karin bayani: Jami'an tsaro sun kamo fursunoni 108 da suka tsere daga gidan yarin Kogi

  • Jami'an tsaro a jihar Kogi sun yi nasarar kamo wasu daga cikin fursunonin da suka tsere daga gidan yari
  • Idan baku manta ba, a jiya ne 'yan bindiga suka farmaki gidan yari, suka saki wasu daga cikin fursunoni
  • A halin yanzu ana ci gaba da bincike don kamo sauran wadanda suka tsere daga gidan na yari

Kogi - Akalla fursunoni 99 daga cikin 294 da suka tsere daga cibiyar gyaran hali ta Kabba da ke jihar Kogi a ranar Litinin 13 ga watan Satumba ne jami’an tsaro suka kamo.

ThisDay ta ba da rahoton cewa a daren Litinin sama da sauran fursunoni 150 ne ba a san inda suke ba bayan da suka tsere. Jaridar da ta ambato wasu majiyoyi inda ta lura cewa wasu daga cikin fursunonin sun dawo bisa radin kansu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tare motar jigon PDP sun yi awon gaba da shi da direbansa

An tattaro cewa wasu bayan sun fahimci mummunan aikin da suka aikata na tserewa sun mika kansu da kansu ga gidan na gyaran hali.

Fashin magarkama: Jami'an tsaro sun kamo fursunoni 99 da suka tsere a Kogi
Fursunoni sun tsere an kamo su | Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Haka kuma hukumar sa-ido ta jihar Kogi ta yi ikirarin cafke wasu fursunoni da 'yan bindiga suka kubutar a cikin daji.

A cewar Haileru Dan Baba, kwanturola janar na hukumar gyaran hali, an fara gudanar da bincike kan lamarin don kamo wadanda suka tsere.

A rahoton da jaridar Punch ta fitar, wani jami'i a hukumar gyaran hali ya bayyana cewa, fursunoni 108 ne jami'an tsaro suka kamo tun bayan tserewarsu.

A cewar mai magana da yawun hukumar gyaran hali na Najeriya ga AFP ta wayar tarho:

"Muna da jimilar fursunoni 108 da aka kamo."

Ya kuma ba da tabbacin cewa, a hankali jami'an tsaro za su kara kamo sauran fursunonin da suka tsere.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun kai farmaki gidan yari, sun saki fursunoni 240 sannan suka kashe sojoji a Kogi

‘Yan bindiga sun kai farmaki gidan yari, sun saki fursunoni 240 sannan suka kashe sojoji a Kogi

Akalla fursunoni 240 ne suka tsere daga Cibiyar Tsaro ta MSCC da ke Kabba, Jihar Kogi, bayan wani hari da ‘yan bindigar da ba a san ko su wanene ba suka kai, Channels TV ta ruwaito.

Mai magana da yawun ma’aikatar gidan yari (NCoS), Mista Francis Enobore ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, inda ya bayyana cewa harin ya faru ne da tsakar daren ranar Lahadi.

A cewarsa, maharan da yawansu sun isa gidan gyara halin dauke da muggan makamai kuma nan da nan suka fafata da masu gadin gidan ta hanyar musayar wuta.

Mista Enobore ya ci gaba da bayyana cewa Kwanturola -Janar, Haliru Nababa ya ba da umurnin a fara aikin kamo su nan take tare da gudanar da cikakken bincike yayin da ya jagoranci wata tawaga don tantance halin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Daliban Zamfara 75 da aka sace sun samu 'yanci bayan kwanaki 11

Nababa ya kuma yi kira ga jama'a da su bai wa jami'an tsaro bayanan sirri masu amfani da za su taimaka wajen kamo wadanda suka tsere.

Jaridar The Nation ta kuma ruwaito cewa an kashe sojoji biyu da ke kan shingen bincike a gaban gidan gyara halin sannan kuma aka jikkata wani a lokacin da maharan suka kai farmaki.

Wata majiya ta tabbatar da cewa daga baya an sake kama wasu daga cikin fursunonin da suka tsare da misalin karfe 8 na safe ranar Litinin a kusa da Otal din Kudon, Kabba, lokacin da suka yi kokarin shiga abin hawa don tserewa zuwa jihar Kwara da ke makwabbtaka.

Sojin Najeriya sun kera motocin da kan iya hango 'yan ta'adda daga nisan tazara

A wani labarin, Babban hafsan sojojin kasa (COAS), Laftanar Janar Farouk Yahaya, a ranar Litinin 13 ga watan Satumba, ya ba da sabbin motocin sadarwa na tauraron dan adam wadanda za a tura su ga rundunoni daban-daban na soji a fadin kasar.

Kara karanta wannan

Binciko Gaskiya: Da gaske ne DSS sun kama telan Buhari da ya yi masa dinkin Imo?

Motocin na dauke da kyamarori da kayan aikin lantarki na zamani, kuma rundunar sojan Najeriya ta Cyber ​​Warfare Command, Abuja ta kirkiresu, The Sun ta ruwaito.

Da yake jagorantar COAS yayin ziyarar duba motocin, Kwamandan, Cyber ​​Warfare Command, Birgediya Janar Adamu, ya ce motocin na hango abu daga nisan kilomita 6.5 kuma an sanya masu na'urorin da za su taimaka a hango abubuwa ko da cikin dare ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel