Damfarar daukar aiki: An dakatar da mataimakin shugaban marasa rinjayen majalisar Nasarawa
- Majalisar Nasarawa ta dakatar da mataimakin shugaban marasa rinjaye na jihar, Luka Zhekaba
- Ana zarginsa da daukar malamai 38 na makarantar sakandare aiki ba bisa ka'ida ba
- Majalisar ta dakatar da shi tare da kafa kwamitin mutum 3 na bincike kan dan majalisar
Lafia, Nasarawa - Majalisar jihar Nasarawa ta dakatar da mataimakin shugaban marasa rinjaye, Luka Zhekaba wanda aka fi sani da PDP-Obi 2 kan zarginsa da ake da daukar aikin bogi na malamai 38 na makarantun sakandare a jihar.
Daily Nigerian ta ruwaito cewa, kakakin majalisar, Ibrahim Abdullahi, ya sanar da wannan yayin zaman majalisar a ranar Litinin a Lafia.
Dakatar da Zhekaba ya zo ne bayan majalisar ta tattauna kan rahoton kwamitin ilimi na majalisar kan daukar aikin malamai 366 da wasu 38 na bogi da aka gani wurin jerin biyan kudin albashi na jihar.
Kakakin majalisar ya kafa kwamitin mutum uku na wucin-gadi domin bincikar dakataccen dan majalisar kuma a kawo rahoto gaban majalisar nan da makonni biyu, Daily Nigerian ta ruwaito.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce:
"Kwamitin ya bukaci dakatar da Honarabul Luka Iliya Zhekaba, mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar kuma a kafa kwamitin wucin-gadi domin bincikar zarginsa da ake da hannu cikin daukar malamai na bogi.
"A don haka na nada kwamitin mutum uku domin bincikar zarginsa da ake da hannu kuma a kawo rahoto gaban majalisar nan da makonni biyu.
“Honarabul Sulaiman Yakubu Azara, dan majalisa mai wakiltar mazabar Awe ta kudu zai zama shugaban kwamitin, Honarabul Usman Shafa, dan majalisa mai wakiltar mazabar Toto/Gadabuke da Honarabul Samuel Tsebe, dan majalisa mai wakiltar mazabar Akwanga ta kudu za su zama mambobin kwamitin wucin-gadin.
“Honarabul Ibrahim Musa, mataimakin magatakardan majalisar, shi ne sakataren kwamitin," yace.
"Ba zan tuhumi hannunsa a ciki ba a yanzu ba har sai kwamitin ya kammala bincikensa. A yayin da kuka fara bincike, ina muku fatan nasara."
Abdullahi ya ce majalisar ba ta sukar daukar aikin malaman, amma ya dace a bi komai yadda ya dace cike da gaskiya.
'Yan bindiga sun sanar min salon da suke bi wurin guje wa luguden sojin sama, Gumi
A wani labari na daban, sanannen malamin addinin Islama mazaunin Kaduna, ya kara tabbatar wa da jama'a cewa a koda yasuhe ya na samun damar tattaunawa da 'yan fashin dajin da suka addabi arewacin Najeriya.
A takardar da malamin ya fitar a cikin kwanakin nan, ya bayyana cewa gungun 'yan bindiga sun sanar da shi cewa luguden ruwan wutan da sojin saman ke yi ba ya taba su, sai dai ya taba matansu da 'ya'yansu, domin kuwa suna da salon kauce musu, Punch ta ruwaito.
Gumi ya ce 'yan bindigan sun kware tare da zama 'yan hannu wurin kauce wa duk wani bam da sojin sama za su wurgo, hakan ne yasa da kyar a iya kama su ko halaka su.
Asali: Legit.ng