Masallacin kasa ya kaddamar da asusun neman tallafin N29bn na ayyuka

Masallacin kasa ya kaddamar da asusun neman tallafin N29bn na ayyuka

  • Hukumar kula da masallacin kasa da ke Abuja ta sanar da neman tallafi da ta ke na kudi domin wasu ayyukan masallacin
  • Kamar yadda Murshid Farfesa Galadanci ya sanar, akwai bukatar masallacin ya tsaya da kansa ba tare da dogaro da kowa ba
  • Don haka ana bukatar gina rukunin shaguna, gidaje, otal da sauran abubuwan da za su samar wa da masallacin kudi kai tsaye

FCT, Abuja - Hukumar kula da masallacin kasa na Abuja ta kaddamar da asusun neman taimakon kudin kula tare da cigaba da ayyukan masallacin, Daily Trust ta ruwaito hakan.

An yi wannan kiran ne yayin wani taron masu ruwa da tsaki cikin kwanakin karshen makon nan da ke Abuja inda aka tattauna kan yadda za a samo kudin domin cigaba da kuma gina wurin kasuwanci na N29 biliyan da sauransu.

Kara karanta wannan

Binciko Gaskiya: Da gaske ne DSS sun kama telan Buhari da ya yi masa dinkin Imo?

Masallacin kasa ya kaddamar da asusun neman tallafin N29bn na ayyuka
Masallacin kasa ya kaddamar da asusun neman tallafin N29bn na ayyuka. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Murshid na masallacin, Farfesa Shehu Galadanci, ya sanar da cewa wannan yunkurin an fara yin shi ne domin a samu 'yanci wurin taimaka wa Da'awah da kuma jin dadin al'ummar Musulmi.

Ya ce a wancan karon da aka nemi tallafin karkashin mulkin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ba a duba nawa ake nema ba wurin zaman masallacin da kansa amma an mayar da hankali wurin gyaran wuraren da suka sukurkuce.

Ya bayyana cewa sun tattauna da Islamic Development Bank (IsDB) domin samun kudin ayyukan amma sun jaddada cewa dole ne a nemi taimako daga Musulmi masu hali.

Ibrahim Bunu, masani a fannin zane wanda shi ne shugaban kwamitin ayyuka, ya ce aikin zai zauna kan fili mai girman kadada 2.2 kuma za a yi shi a kashi 3.

Kara karanta wannan

Yanzu yanzu: Buhari ya gindaya sharuddan biyan albashin likitoci, ya soki yajin aiki

Tsohon ministan tarayya ya bayyana cewa za a yi amfani da filin wurin gina gidajen zama, ofisoshi, otal da sauransu wadanda za su iya samarwa da masallacin kudi.

Ya bayyana cewa kashin farko za a fara da rukunin shaguna saboda zai iya zama babban aiki idan aka ce a lokaci daya za a yi, Daily Trust ta wallafa.

A bangarensa, Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III, ya yi kira ga Musulmin Najeriya da su tallafa wurin tabbatar da aikin ya samu nasara.

Shugaban sojin sama: Luguden da sojoji ke wa 'yan ta'adda ya na haifar da sakamako mai kyau

A wani labari na daban, Oladayo Amao, shugaban dakarun sojin sama, ya ce lugude da ayyukan sojoji kan 'yan ta'adda ya na bada sakamako mai kyau.

Kamar yadda TheCable ta ruwaito, takardar da Edward Gabkwet, mai magana da yawun NAF ya fitar, Amao ya sanar da hakan ne yayin da ya kai ziyara ga dakarun da ke Maiduguri na da Yola.

Kara karanta wannan

Nasara: 'Yan bindiga sun gurzu, suna rokon jama'a yafiya tare da sako wadanda suka sace a Zamfara

Dakarun suna daga cikin jami'an operation Hadin Kai, tsohuwar rundunar operation Lafiya Dole.

A yayin ziyarar, Amao ya samu bayani daga Nnamdi Ananaba inda ya bada takaitaccen bayani kan manyan nasarorin da sojin saman suka samu wurin dakile ta'addanci a jihar Borno, balle a kwanaki talatin da suka gabata.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel