Mai da tsohuwa yarinya: Bidiyon yadda 'yan kwalliya suka sauya halittar tsohuwa

Mai da tsohuwa yarinya: Bidiyon yadda 'yan kwalliya suka sauya halittar tsohuwa

  • Ashe kwalliya na iya sauya tsohuwa ta koma budurwa? Wannan wani bidiyo ne da ya tabbatar da haka
  • An samu wani bidiyo da wata tsohuwa ke cancara kwalliya, inda ta canza kamanni zuwa wata kyakkyawar budurwa
  • Mutane da dama sun yi tsokaci akai, inda wasu ke ganin ko babu kwalliya tsohuwar kyakkyawa ce

Wani bidiyon da aka yada kafafen sada zumunta na wata tsohuwa tana kwalliya ya bar baya da kura, inda mutane da yawa suka ji mamakin yadda tsohuwar ta canza zuwa kyakkyawar budurwa.

A cikin bidiyon da @arewafamilyweddings ya yada a shafin Instagram, matar ta zauna kan kujera yayin da mai mata ke mata kyakkyawan kwalliyar a fuskarta.

Mai da tsohuwa yarinya: Bidiyon yadda 'yan kwalliya suka sauya halittar tsohuwa
Hotunan tsohuwar da aka yiwa kwalliya | Hoto: @arewafamilyweddings
Asali: Instagram

Kalli bidiyon:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tare motar jigon PDP sun yi awon gaba da shi da direbansa

Martanin mutane game da bidiyon

Da yawa daga cikin masu amfani sada zumunta na Instagram ba da jimawa ba sun mamaye sashen sharhi bidiyon da aka yada. Wasu daga cikin wadanda suka yi tsokaci sun ce tsohuwar kyakkyawa ce ko da ace bata yi kwalliya ba.

Mai amfani da Instagram tare da riko @mzz_khennie ya ce:

"Tana da kyawunta ko da ba tare da kwalliya ba."

@mhiz_kdee ya rubuta:

"Matsalar yanzu ita ce kaka ta ba za ta yarda ta yi kwalliya ba."

A sharhin @minalsfoods:

"Toh fa. Tsohuwa taji jiki kam. Kawai kuna wahala tsohuwar da bata ji ba bata gani ba."

@prettyhajiascollection ya rubuta:

"Soooo Pretty."

Shekaru 35 yana aikin koyarwa a Borno, dan Najeriyan da Turawa suka horar ya koma talla

A wani labarin, Bayan shekaru 35 yana hidimar aikin gwamnati a matsayin malamin makaranta a jihar Borno, wani dan Najeriya ya koma talla a kan titi don samun abin biyan bukata.

Kara karanta wannan

Binciko Gaskiya: Da gaske ne DSS sun kama telan Buhari da ya yi masa dinkin Imo?

An ga Al-Amin Shettima Bello wanda ya yi ritaya daga aikin koyarwa yana tafe yana tallan man zafi da aka fi sani mantileta a Maiduguri, Daily Post ta ruwaito.

Hanyar da Bello ke bi wajen samun na abin ka ya kasance yana zama a kusa da cibiyar ATM ta Bankin First Bank a Monday Market ta Maiduguri don kwastomomi daga masu zuwa da banki ko ATM.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Tags: