‘Yar Jafar Mahmud Adam ta haihu, an rada wa yaro sunan 'danuwanta da ya rasu a hadarin mota

‘Yar Jafar Mahmud Adam ta haihu, an rada wa yaro sunan 'danuwanta da ya rasu a hadarin mota

  • Labari ya zo cewa Malama Zainab Jafar Mahmud Adam ta haifi yaro
  • Mahaifinsa, Ibrahim Rijiyar Lemu ya rada wa jariri suna Abdulmalik
  • Jinjirin ya dauki sunan kawunsa da ya mutu a sanadiyyar hadari a 2020

Kano - A tsakiyar makon nan ne muka samu labari cewa babbar ‘diyar marigayi Sheikh Jafar Mahmud Adam watau Zainab, ta samu karu wa.

Legit.ng ta samu labarin wannan haihuwa ne a shafin Zainab Jafar Mahmud na Facebook, inda ta bada sanarwar a ranar 7 ga watan Satumba, 2021.

Allah ya sa ya fi mu a komai - Mansur Sokoto

Shehin malami, Farfesa Mansur Sokoto ya tabbatar da labarin wannan karu wa da Dr. Ibrahim Rijiyar Lemo da Zainab Jafar Mahmud suka samu.

Babban malamin yake cewa sun samu karin jika, ya kuma yi addu’a ga Ubangiji ya yi wa yaron albarka, sannan ya kare shi daga fitintinun zamani.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Jami'in dan sanda ya harbe abokin aikinsa dan sanda a jihar Kano

Malama Zainab Jafar Mahmud ta gode wa ‘yanuwa da suka taya ta da addu’o’i da fatan alheri, ta bayyana cewa an sa wa yaron suna Abdul Malik.

‘Yar 'yar Jafar Mahmud Adam
Abdulmalik Ibrahim Rijiyar Lemu Hoto: Zainab Ja'afar Mahmud
Asali: Facebook

Zainab Jafar Mahmud ta bada sanarwa

Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuhu.
Ina miqa godiya ta musamman ga iyaye, 'yan uwa, na kusa da na nesa bisa ga addu'o'in alkhairi, taya murna da kyakkyawan fata da suke ta aikowa bisa ga samun karuwa da mu ka yi ta Abdul-Malik Ibrahim Abdullahi.
Ina fatan Allah Ya amsa addu'o'inku Ya kuma sanya a mizanin alkhairi, Allah Ya azurta mu baki-daya da zuriyya mai albarka da Annabi s.a.w zai yi alfahari da ita ranar Alqiyama amin.
Jazakumullahu Khairan.

Kusan shekara daya da ta wuce aka samu labari mara dadi na mutuwar AbdulMalik, daya daga cikin ‘ya ‘yan da Ja'afar Mahmud Adam ya bari a Duniya.

Kara karanta wannan

Babu shakka Buhari da 'yan Najeriya za su yi farin ciki da mu, Sabon Ministan lantarki

Mahaifin wannan jariri, Dr. Ibrahim Rijiyar Lemu ya rada masa sunan baffansa da ya rasu. Muna addua'a Allah ya jikan wadanda suka rasu, ya raya yaron.

An sa wa Jikan Sheikh Jafar suna Jafar

Idan ba ku manta ba a cikin watan Azumi ne Salim Jafar Mahmud Adam ya bada sanarwar cewa shi ma Mai dakinsa ta haihu, ya sa wa yaron suna Jafar.

Malam Salim Jafar Adam kani ne a wurin mai jego, Zainab Jafar Mahmud Adam. Dukkaninsu ‘ya ‘yan bajimin malamin nan ne da aka kashe a Kano a 2007.

Asali: Legit.ng

Online view pixel