Gwarazan Yan Sanda Sun Ragargaji Mayakan IPOB, Sun Hallaka Kwamanda da Wasu da Dama

Gwarazan Yan Sanda Sun Ragargaji Mayakan IPOB, Sun Hallaka Kwamanda da Wasu da Dama

  • Rundunar yan sanda reshen jihar Imo, ta sanar da cewa jami'anta sun ragargaji sansanin mayakan haramtacciyar kungiyar ESN/IPOB
  • Kakakin yan sandan Imo, CSP Michael Abattam, yace jami'an sun hallaka wani kwamandan kungiyar
  • A cewarsa, yayin musayar wutar da aka yi, jami'an yan sanda sun sheke mutum uku, sun cafke biyu yayin da sauran suka tsere

Imo - Rundunar yan sanda reshen jihar Imo, ta bayyana cewa jami'ai sun ragargaji wani sansanin mayakan kungiyar awaren IPOB, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Kakakin rundunar, CSP Michael Abattam, shine ya bayyana haka a Owerri, babban birnin jihar Imo.

Yace wannan nasarar na ɗaya daga cikin yakin da rundunar take domin kakkabe ragowar mayakan haramtacciyar ƙungiyar da suka rage.

Gwarazan yan sandan sun lalata sansanin mayakan ESN/IPOB dake Amaifeke, karamar hukumar Orlu, jihar Imo.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: An toshe hanyoyin sadarwa na zamani a jihar Katsina

Gwarazan Yan Sanda Sun Ragargaji Mayakan IPOB
Gwarazan Yan Sanda Sun Ragargaji Mayakan IPOB, Sun Hallaka Kwamanda da Wasu da Dama Hoto: thisdaylive.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mun sami bayanan sirri masu karfi kan yan ta'addan

Abattam ya bayyana cewa jami'an yan sanda sun samu bayanan sirri cewa an hangi yan ta'addan IPOB na taruwa a wani gini da ba'a ƙarisa ba, inda suke kitsa shirin kaiwa jami'an tsaro hari.

A sanarwar da ya fitar, kakakin yan sandan yace:

"A ranar 11 ga watan Satumba da misalin karfe 12:30 na rana, tawagar yan sanda ta mamaye maɓoyar kungiyar yan ta'addan dake wani gini da ba'a ƙarisa ba a wanda aka fi sani da Ngbuka, Amaifeke, karamar hukumar Orlu."
"Yayin da yan ta'addan suka ga jami'an tsaro sun musu dirar mikiya sai suka buɗe musu wuta amma sai gwarazan yan sandan suka maida martani nan take."
"A wannan musayar wuta ne uku daga cikin yan ta'addan suka mutu, daga cikinsu akwai kwamandan ƙaramar hukumar Orlu, Chidera Nnabuhe."

Kara karanta wannan

Ba zama: 'Yan sanda sun ci alwashin kamo wadanda suka sace ma'aikatan Obasanjo

Shin jami'an yan sanda sun kame wasu?

The Cable ta ruwaito cewa yan sandan sun samu nasarar cafke mutum biyu, Emeka Sunday da kuma Anthony Okeke, yayin da sauran suka tsere da raunuka a jikinsu.

A wani labarin kuma Al'ummar Sokoto Sun Shiga Tashin Hankali Yayin da Yan Bindiga Suka Aike Musu Wasikar Barazana

Yan bindigan da suka gudo daga jihar Zamfara , waɗanda suka kai hari kan kauyukan dake bakin boda a Sokoto makon da ya shuɗe, sun aike da wasikar cigaba da miyagun ayyukansu ga mutanen yankin.

Lamarin ya jefa mutanen yankunan cikin tashin hankali da zaman ɗar-ɗar kan yaushe maharan zasu shigo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262