Marwa: NDLEA ta kwace miyagun kwayoyi na N6bn masu alaka da ISIS

Marwa: NDLEA ta kwace miyagun kwayoyi na N6bn masu alaka da ISIS

  • Shugaban hukumar yaki da safarar miyagun kwayoyi ta NDLEA, Buba Marwa ya bayyana yadda suka kwace miyagun kwayoyi masu kimar naira biliyan 6
  • A ranar Laraba yayin wani taro, ya bayyana yadda suka kama miyagun kwayoyi a filin jirgin ruwa da ke Apapa, jihar Legas wanda aka turo daga gabas ta tsakiya
  • A cewar sa, miyagun kwayoyin masu suna Captagon suna da alaka da kungiyoyin ‘yan ta’adda da ke gabas ta tsakiya kuma NDLEA ta samu bayanan sirri kan su

Lagos - Shugaban hukumar yaki da safarar miyagun kwayoyi ta NDLEA, Buba Marwa, ya bayyana yadda suka kwace miyagun kwayoyi masu kimar naira biliyan 6 a filin jirgin ruwa da ke Apapa, jihar Legas.

TheCable ta ruwaito cewa, ya yi wannan jawabin ne a ranar Laraba inda shugaban NDLEA din ya ce kwayoyin sun zo ne daga gabas ta tsakiya.

Kara karanta wannan

Hisbah Ta Kama Motoci Biyu Maƙare Da Katon Ɗin Giya 5,760 a Kano

Marwa: NDLEA ta kwace magunguna karin karfin maza na N6bn masu alaka da ISIS
Marwa: NDLEA ta kwace magunguna karin karfin maza na N6bn masu alaka da ISIS. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

A cewarsa, hukumar ta samu bayanan sirri ne daga abokan huldar ta dangane da safarar kwayoyi ta filin jirgin Apapa.

Marwa ya ce kwayoyin masu suna Captagon suna da alaka da kungiyar ‘yan ta’adda da ke gabas ta tsakiya, TheCable ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“A watan Maris din 2021, mun samu bayanan sirri daga abokan huldar mu na batun safarar miyagun kwayoyi a Najeriya daga gabas ta tsakiya ta filin jirgin kasa na Apapa.
"Kayan sun wuce ta kasashe 3 sannan suka iso kasar arewacin Afirka amma muka cigaba ta bin kayan,” kamar yadda takardar ta zo wacce Femi Babafemi ya saki.
“A ranar Alhamis 26 ga wata. Augusta muka fara bi takan kayan inda muka ga wasu injinan gyara gilasai da sauran su.
“A ranar Litinin 31 ga watan Augusta muka ci gaba da bincike ta hanyar anfani da karen mu, sai muka gane kayan suna cikin daya daga cikin injinan. Washegari, 1 ga watan Satumba muka ga kwayoyin Captagon 18,560 masu nauyin 3.2kg da aka boye a wayoyin injin din.

Kara karanta wannan

Yan fashi sun taremu a hanya, sun kwace takardun kotu hannunmu, Lauyoyin DSS ga Alkali

A ranar 2 ga watan Satumba, mun sake bude ijinan 2 kuma mun samu kwayoyi 451, 807 masu nauyin 74.119Kg a cikin kwayel din.
Idan muka duba darajarsu a gari, kowacce kwaya ana siyar da ita kan dala 25. Mai su zai iya siyar da su kan dala miliyan 11.3 daidai da biliyan shida.

Buba Marwa ya kara da bayyana cewa, wannan ne karo na farko da aka taba shigowa da kwayar wata kasar Afrika kuma an yi hakan ne saboda 'yan ta'adda.

'Yan bindiga sun sheke rayuka 300, mutum 3,000 sun rasa muhalli a Niger ta gabas, Sanata

A wani labari na daban, Sanata mai wakiltar Neja ta arewa a majalisar tarayya, Mohammed Sani-Musa, a ranar Talata ya bayyana cewa ‘yan bindiga sun hallaka fiye da rayuka 300 sannan sun hana fiye da mutane 3000 zama a gidajensu a cikin mazabar sa cikin watanni kadan da suka gabata.

Kara karanta wannan

Usman Baba Alkali: Na zama IGP a lokacin da a ke tsaka da fuskantar jarabawa

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, a wata takarda da Sani-Musa ya saki a ranar Talata a Minna ta jihar Neja, ya kwatanta ayyukan ‘yan bindigan a matsayin zalunci da mugunta ga dan Adam.

A cewar sa:

“A cikin watanni biyu da suka gabata, a kalla mutane 3000 ne suka rasa gidajensu suka koma zama a sansanin ‘yan gudun hijira ,sannan sun yi asarar dukiyoyin su masu yawan gaske ta hanyar kwace ko kuma a lalata su."

Asali: Legit.ng

Online view pixel