Yajin aiki: FG ta ce babu likitan da ke bin ta ko naira daya
- A ranar Talata gwamnatin tarayya ta musanta zancen da ke cewa gwamnatin tarayya ta na rike da albashin likitoci da sauran ma’aikatan lafiya
- Ministan kwadago da ayyuka, Chris Ngige ya bayyana hakan a wani taro na kwamitin fadar shugaban kasa a kan albashi da shugabannin JOHESU
- Ngige ya ce karairayin kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta NARD ta na toshe wa mutane ganin kokarin gwamnatin tarayya dangane da harkokin lafiya
Abuja - Gwamnatin tarayya a ranar Talata ta musanta batun da ke cewa ta na rike da albashin likitoci da sauran ma’aikatan lafiya inda ministan kwadago ya ce zancen kanzon kurege ne.
Daily Trust ta ruwaito cewa, ministan kwadago da ayyuka, Chris Ngige ya bayyana hakan a wani taro na kwamitin gwamnatin tarayya a kan albashi tare da shugabannin kungiyoyin ma’aikatan lafiya.
Ngige ya ce, wadannan karairayin daga kungiyar likitoci masu neman kwarewa ne ta NARD, wadanda suke hana kowa ganin kokarin gwamnatin tarayya a kan harkar lafiya.
“NARD ta tafi ta na yada cewa gwamnatin tarayya ta na rike da albashin su kuma ba ta daukar matsalolin lafiya da muhimmancu. Wannan ba gaskiya ba ne.
“Kungiyar NARD ta ki sanar da likitoci cewa wadanda suke bin gwamnatin tarayya albashi su ne wadanda aka dauka lokacin da bai dace ba don haka gwamnatin tarayya ba ta san da su ba kuma ofishin kasafi ba sa kididdiga da su.
“Ana kasafin albashin ko wanne wata ne ga wadanda gwamnatin tarayya ta yarda ta dauka aiki da kuma wadanda gwamnati takan dauka don suyi aiki na lokaci zuwa lokaci kuma tana kirge ‘yan kudaden su ta biya su. Kuma hakan ya na daukar lokaci ba dare daya ake yi ba,” a cewar ministan.
Ngige wanda shine mai magana da yawun shugaban kasa a harkar ayyuka, ya tabbatar wa da likitocin da gwamnati ta amince da daukar su za su samu kudaden su cikin kwanciyar hankali.
Ya tabbatar da cewa kudaden da likitoci da wasu ma’aikatan lafiya suke bin gwamnatin tarayya kudade ne na alawus din COVID-19 na shekarar 2020, kuma kusan ko wacce ma’ikata an samu irin haka.
Ya ce yanzu haka suna ayyuka tukuru wurin ganin an gyara komai, Daily Trust ta ruwaito.
A bayanan da yayi, karamin ministan lafiya, Sanata Olorunnimbe Mamora, ya ce bai dace a je yajin aiki a halin da ake ciki ba yanzu, duk da gwamnati ta mayar da hankalinta wurin ganin ta biya likitoci da sauran ma’aikatan lafiya albashin su.
Karamin ministan kudi, kasafi da tsari, Clement Agba ya ce duk da halin rashi da kasa ta ke ciki, gwamnatin tarayya ta na iyakar kokarin ganin ta samar wa da matasa walwala.
A cewar sa, gwamnati ba za ta cigaba da rancen kudi ta na biyan albashi ba.
Shugaban JOHESU, Josiah Biobelemonye ya ce kungiyarsa ce damo sarkin hakuri a duk bangarorin lafiya, inda yace a rage matsa wa ma’aikatan don gudun su fusata su fara yajin aiki.
Mulki na ya shirya bai wa rayuka da kadarorin 'yan Najeriya kariya, Buhari
A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara tabbatar wa da ‘yan Najeriya tabbacin sa na cewa mulkin sa zai tabbatar da tsare rayuka da dukiyoyin duk wasu ‘yan Najeriya ko menene matsayinsa a kasar nan.
Daily Nigerian ta ruwaito cewa, ministan tsaro, Bashir Magashi ya ce Shugaban kasa ya bayyana hakan a wani taro na tsaron kasa wanda suka yi a fadar shugaban kasar da ke Abuja a ranar Talata.
Magashi ya bayyana hakan inda yace shugabannin tsaro sun kara bayyana halin da kasar nan ta ke ciki na rashin tsaro har da sabon ta’addancin da ya faru a jihar Zamfara da sauran jihohi na arewa maso yanma da arewa ta tsakiya da ke fadin kasar nan, Daily Nigerian ta ruwaito hakan.
Asali: Legit.ng