An kama fasto da ta mayar da coci gidan da ake ɗirka wa mata ciki suna haihuwar jarirai ana sayarwa attajirai

An kama fasto da ta mayar da coci gidan da ake ɗirka wa mata ciki suna haihuwar jarirai ana sayarwa attajirai

  • Hukumar ‘yan sandan jihar Imo ta kama wata fasto da wasu mutane 4 wadanda suka mayar da coci wurin sayar da jarirai
  • A cikin cocin dake titin MCC/Uratta, karamar hukumar Owerri ta arewa suke satar ‘yan mata, a dirka musu ciki, su haihu, sannan a sayar da jariran
  • An samu nasarar kamo faston da sauran ‘yan uwan harkar ta a ranar 8 ga watan Satumba da misalin karfe 8:30 na safe bayan samun bayanan sirri akan su

Jihar Imo - Rundunar ‘yan sandan jihar Imo sun kama wata fasto da sauran mutane 4 da ake zargin sun mayar da coci kasuwar jarirai, rahoton News Wire NGR.

Rahoton LIB ya ce ‘yan sanda sun afka wa cocin wacce take a kan titin MCC/Uratta a karamar hukumar Owerri ta arewa bayan samun wasu bayanan sirri akan abubuwan da suke guduna a cikin ta.

Kara karanta wannan

Hotunan mutumin da aka kama ya damfari mutane 64 miliyoyin naira a Kano

An kama malamar coci da ta mayar da coci gidan da ake yi wa mata ciki suna haihuwar jarirai da ake sayarwa
Malamar coci da mukarrabanta da aka kama sun mayar da coci wurin yi wa mata ciki don su haifa jarirai na sayara a Imo. Hoto: News Wire NGR
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tushen lamarin

Kamar yadda wata takarda wacce kakakin rundunar, Micheal Abattam, ya saki a ranar 8 ga watan Satumba, ‘yan sanda sun samu wasu rahotanni na sirri akan batar wata Amarachi Okechukwu Dioku mai shekaru 18, ‘yar Umudurualaoka Uba Afakala dake karkashin karamar hukumar Mbaitoli ta jihar Imo a ranar 23 ga watan Mayun 2021 amma aka gan ta a cikin cocin.

Kamar yadda takardar ta zo, bayan samun rahoton, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Rabiu Hussaini ya tayar da rundunar yaki da garkuwa da mutane ta nufi cocin ‘Jesus Life Assembly’.

Nan take aka kama Ugochi Orisakwe, matar dake zama a cikin cocin tare da Chidi Orisakwe, Pauline Nwagbunwanne, Elizabeth Uzoma da Chibueze Joy, abokan harkar ta, aka kwashe su zuwa ofishin ‘yan sanda.

An samu nasarar ceto wata yarinya daga hannun su

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun far ma matafiya, sun yi garkuwa da mutum 5 a Ondo

“An ceto yarinyar da ake nema inda ka ganta da juna biyu mai watanni 5 take anan aka wuce da ita asibitin gwamnati don duba lafiyar ta. Daga baya aka mika ta hannun iyayen ta wadanda suka cika da farin ciki,” kamar yadda takardar ta zo.

Abinda faston ta bayyana bayan ta sha lugude wurin ‘yan sanda

“Bayan an tambayi faston, ta bayyana cewa tana amfani da cocin ne a matsayin wurin ajiye ‘yan mata, a dirka musu ciki sannan su haihu. Bayan nan sai ta biya su ta kuma sayar da yaran ga abokan harkarta da basu taba haihuwa ba.”

Yanzu haka hukumar ‘yan sanda tana cigaba da bincike akan faston da abokan harkar ta.

Wani mutum ya gamu da ajalinsa yayin da ya shiga maƙabartar musulmi cikin dare don haƙo gawa

A wani labarin daban, wani mutum da ba a gano ko wanene ba ya mutu yayin da ya ke yunkurin hako gawa a makabarta da ke Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan bindiga sun sace ma'aikatan Obasanjo 3 bayan yi wa motarsu luguden wuta

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a makabartar musulmi da ke Iberekodo, karamar hukumar Abeokuta ta Arewa na jihar Ogun.

Abimbola Oyeyemi, mai magana da yawun yan sandan jihar Ogun, ya tabbatarwa Premium Times afkuwar lamarin a ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel