Da sauran kwana a gaba, bindigar ‘Dan sanda ta kusa kashe Sanata Uba a wajen kamfe
- Bindiga ta tashi a lokacin da Sanata Andy Uba yake kamfe a garin Aguata
- Ana zargin wani ‘dan sanda ne da ya sha giya, ya saki kunamar bindigarsa
- Hakan ya gigita mutane wajen kamfe, sai dai lamarin bai zo da tsautsayi ba
Anambra - Ubangiji ya hukunta ‘dan takarar APC a zaben gwamnan Anambra, Andy Uba yana da sauran kwana, da yanzu wani labarin ake yi dabam.
Jaridar Punch tace saura kiris a bindige Sanata Andy Uba yayin da ya je yawon kamfe a garin Aguata a ranar Juma’a, 5 ga watan Satumba, 2021.
Andy Uba yana yi wa magoya baya da mutanen gari kamfe a filin wasa na Ekwulobia da ke karamar hukumar Aguata yayin da bindiga ta tashi.
Bindigar wani ‘dan sanda ta tashi ana tsakiyar taro, harsashin ya fita zuwa daidai inda Sanata Uba yake tsaye, yana magana da dandazon al’umma.
Rahoton yace wannan abu da ya faru ya girgiza mutanen da suka zo wajen domin su hadu da ‘dan takarar jam’iyyar APC a zaben 6 ga watan Nuwamba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Meya faru mutumina?
Da ‘dan takarar gwamnan ya ji karar bindiga ta tashi daf da inda yake tsaye, sai ya rude, aka ji ya fara kiran; ‘Mutumi na menene wannan? Meya faru?”
Wani ‘dan jarida da komai ya faru a gaban idanunsa, ya bayyana cewa ana zargin ‘dan sandan da ya yi wannan danyen aiki, ya je ya yi tatul ne da giya.
Daga cikin wadanda suke wurin a lokacin da abin ya faru, akwai wanda ya shaida wa menama labarai cewa hadari aka samu, kunamar ta tashi kwatsam.
Da sauran kwana a gaba
Inda aka yi dace shi ne babu wanda ‘dan sandan ya dana wa dalma, da an samu rauni ko an mutu. Daga baya Sanata Uba ya cigaba da yakin neman zabensa.
Idan babu namijin da ya furta maki so, ki yi amfani da asiri, wata budurwa ta bayar da shawara a bidiyo
Wani babban jami’in ‘dan sanda da yake wurin a lokacin da abin ya faru ya tabbatar da cewa za a binciki lamarin, kuma a hukunta wanda aka samu da laifi.
Rahoto yana zuwa inda aka ji masu fashin baki sun fede lissafin da wasu ‘Yan siyasan Arewa ke yi na tafiya da Goodluck Jonathan a zabe mai zuwa na 2023.
Ana ganin muddin Jonathan ya karbi tayin APC, ya yi mata takarar shugaban kasa har ya ci nasara, 'Yan Arewa za su karbe shugabancin Najeriya a 2027.
Asali: Legit.ng