Zamfara: 'Yan fashin daji sun mayar da ajujuwar makarantu mafakarsu

Zamfara: 'Yan fashin daji sun mayar da ajujuwar makarantu mafakarsu

  • Sakamakon luguden da 'yan fashin daji suka ji na ruwan wuta daga sojojin Najeriya, sun fara tserewa daga dajika
  • An gano cewa sun fara neman mafaka a makarantun firamare na fadin jihar da aka rufe saboda rashin tsaro
  • Sai dai mazauna yankunan da suke boyewar, sun ce hatta a makarantun firamaren ba su tsira ba, ana ragargazarsu

Zamfara - 'Yan fashin daji da ke addabar jama'a mazauna Zamfara kuma fitinarsu ta sa aka rufe makarantu a jihar, sun fara mayar da ajujuwan makarantu zuwa mafakarsu a jihar arewa maso yamman.

Daily Trust ta binciko yadda makarantun firamare masu yawa a yankunan karkarar da suka addaba suka zama wurin kwanan 'yan ta'addan.

Zamfara: 'Yan fashin daji sun mayar da ajujuwar makarantu mafakarsu
Zamfara: 'Yan fashin daji sun mayar da ajujuwar makarantu mafakarsu. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Tun baya, malamai da dalibai sun tattara komatsansu sun koma gida sakamakon al'amuran miyagun da ya hana su sakat.

Kara karanta wannan

‘Yan Taliban suna raba ‘yan mata da maza a Makarantun kasar Afghanistan

Kamar yadda mazauna yankin suka tabbatar, wasu miyagun 'yan bindiga sun taba tare shugaban wata makarantar firamare a karamar hukumar Birnin Magaji inda suka bukaci ya tashi dalibai saboda za su yi bacci a ajujuwan.

Ba tare da bata lokaci ba, kuma da sanin cewa rashin bin wannan umarni zai iya haifar da matsalar, shugaban makarantar tuni ya sallami dalibai.

Daily Trust ta gano cewa, wasu daga cikin 'yan bindigan sun sheka lahira bayan sun tsere tare da boyewa a ajujuwan makarantun firamare na jihar.

Baya ga haka, akwai makarantun da rashin malamai ya addabesu saboda ko an tura sabbin malamai, ba su zuwa saboda tunanin hatsarin da za su saka kan su.

Wannan lamarin ne yasa aka bar makarantun ba tare da amfani da su ba.

Kara karanta wannan

Daga Zamfara zuwa Kaduna: Jirgin yakin NAF ya kone sansanin 'yan bindiga, an kashe 50 a dajin Kawara

Mulki na ya shirya bai wa rayuka da kadarorin 'yan Najeriya kariya, Buhari

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara tabbatar wa da ‘yan Najeriya tabbacin sa na cewa mulkin sa zai tabbatar da tsare rayuka da dukiyoyin duk wasu ‘yan Najeriya ko menene matsayinsa a kasar nan.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, ministan tsaro, Bashir Magashi ya ce Shugaban kasa ya bayyana hakan a wani taro na tsaron kasa wanda suka yi a fadar shugaban kasar da ke Abuja a ranar Talata.

Magashi ya bayyana hakan inda yace shugabannin tsaro sun kara bayyana halin da kasar nan ta ke ciki na rashin tsaro har da sabon ta’addancin da ya faru a jihar Zamfara da sauran jihohi na arewa maso yanma da arewa ta tsakiya da ke fadin kasar nan, Daily Nigerian ta ruwaito hakan.

Kara karanta wannan

Nasara: 'Yan bindiga sun gurzu, suna rokon jama'a yafiya tare da sako wadanda suka sace a Zamfara

Asali: Legit.ng

Online view pixel