Bayan mako 3 da auren dole, mata mai shekaru 19 ta sheƙe mijin ta a Adamawa

Bayan mako 3 da auren dole, mata mai shekaru 19 ta sheƙe mijin ta a Adamawa

  • Rundunar 'yan sandan jihar Adamawa ta cafke wata matashiyar matar aure mai shekaru 19 a duniya da laifin kisan kai
  • Ana zargin Rumasau Muhammad da soka wa mijin ta mai suna Muhammad Adamu wuka bayan mako 3 da aurensu
  • An gano cewa, auren dole aka yi tsakanin ma'auratan biyu, lamarin da yasa ta nemi saki amma ya ki, hakan yasa ta sheke shi

Adamawa - Rundunar 'yan sandan jihar Adamawa ta ce jami'an ta sun yi ram da wata Rumasau Muhammed mai shekaru 19, wacce ake zargi da soka wa wani Muhammed Adamu wuka har ya mutu wanda kuma mijin ta ne.

Kamar yadda 'yan sandan suka sanar, wacce ake zargin na zama ne a kauyen Wuro Yanka da ke karamar hukumar Shelleng a jihar Adamawa, kuma ta aura mamacin a ranar 6 ga watan Augustan 2021 ba da son ran ta ba, TheCable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi: Tura sojoji su ragargaji 'yan bindiga ba zai magance rashin tsaro ba

Bayan mako 3 da auren dole, mata mai shekaru 19 ta sheƙe mijin ta a Adamawa
Bayan mako 3 da auren dole, mata mai shekaru 19 ta sheƙe mijin ta a Adamawa. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Bayan wani lokaci, matashiyar mai shekaru 19 ta bukaci saki daga wurin mijin ta mai shekaru 35, wanda ya ki.

'Yan sanda sun ce a ranar Laraba, hukuncin mijin ya fusata wacce ake zargi inda ta yi amfani da wuka ta soka mishi a ciki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An gano cewa, mamacin ya fadi kasa baya ciki hayyacinsa kuma an mika shi asibiti inda aka tabbatar da rasuwar shi.

Kamar yadda TheCable ta wallafa, matashiyar mai shekaru 19 ta shiga hannun 'yan sanda bayan wani Jophas Johnsely, abokin mamacin, ya kai rahoton abinda ya faru.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Adamawa, Aliyu Adamu, ya umarci 'yan sanda da su bazama bincike kan lamarin yayin da ya shawarci jama'a da su kiyaye tare da daina yi wa 'ya'yansu auren dole.

Babu shakka Buhari da 'yan Najeriya za su yi farin ciki da mu, Sabon Ministan lantarki

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan bindiga sun balle gida, sun sace mata da yaran ta mata 2 a Abuja

A wani labari na daban, sabon ministan wutar lantarki, Injiniya Abubakar D. Aliyu, ya bayyana burinsa na yin aiki tare da duk ma’aikatansa don faranta wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ‘yan Najeriya rai.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Injiniya Aliyu ya sanar da manema labaran gidan gwamnati hakan bayan kammala taro da shugaba Buhari a fadar sa da ke Abuja a ranar Talata.

Ministan ya ce ya je fadar ne musamman don su tattauna da Buhari a kan yadda zai tafiyar da ayyukan sa inda yace, idanun ‘yan Najeriya yana kan ma’aikatar sa kuma za su bukaci ganin wani abu mai kyau da zai fito daga nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel