'Yan bindiga sun shiga 3: NAF ta fara gwada sabbin jiragen Super Tucano

'Yan bindiga sun shiga 3: NAF ta fara gwada sabbin jiragen Super Tucano

  • Yayin da miyagun jihohin Zamfara da na Kaduna ke karba luguden wuta, Najeriya ta cigaba da gwada sabbin jiragen yakin ta
  • Kamar yadda ministan tsaro, Janar Bashir Magashi mai ritaya ya sanar, ana gwada jiragen Super Tucano da Najeriya ta siya daga Amurka
  • An gano cewa jiragen na iya ayyukan leken sirri, sintiri tare da kiyasta tazarar da za su saki bam yayin da suke sama

Aso Villa, Abuja - Yayin da jiragen yakin Najeriya ke cigaba da luguden wuta kan 'yan fashin daji a jihohin Zamfara da Kaduna, rundunar sojin sama ta Najeriya na gwada sabbin jiragen Super Tucano da Najeriya ta siya kwanan nan.

PRNigeria ta ruwaito cewa, ministan tsaro, Janar Bashir Magashi mai ritaya ya bayyana hakan ga manema labarai bayan sa'o'i da suka kwashe suna taro kan tsaron kasa da shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda aka yi da hafsoshin tsaron kasa a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Magashi: 'Yan fashin daji sun zama fitina, 'yan Najeriya ba su yarda za mu iya maganinsu ba

'Yan bindiga sun shiga 3: NAF ta fara gwada sabbin jiragen Super Tucano
Ministan Tsaro, Bashir Magashi tare da shugaban hafsin sojin kasa. Hoto daga PRNigeria.com
Asali: UGC

Kamar yadda Magashi ya ce, za a samu karin jiragen A-29 Super Tucano masu saukar angulu da za su iso nan da mako mai zuwa bayan isowar kashin farko wadanda yanzu a ke gwadawa.

Ministan ya ce taron tsaron da suka yi da shugaban kasa ya sake duba halin tsaron kasar nan kuma sun yanke shawarar cewa, za a shawo kan matsalar tsaron, ballantana a jihar Zamfara da arewa ta tsakiya wanda ya zama gagarumin lamarin da suka tattauna a taron kuma ake neman hadin kan 'yan Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Taron tsaron ya samu shugabancin shugaban kasa yayin da shugaban ma'aikatan tsaro, Janar Lucky Irabor da sauran hafsoshin tsaro suka yi wa shugaban kasa bayani kan cigaban da ake samu tattare da kalubalen tsaron da kasar nan ke fuskanta.

An yi shagalin zuwan jiragen Super Tucano daga Amurka a ranar 31 ga watan Augustan 2021 a Abuja inda manyan hafsoshin soji daga Amurka suka samu damar halarta.

Kara karanta wannan

Mulki na ya shirya bai wa rayuka da kadarorin 'yan Najeriya kariya, Buhari

Wannan shagalin kuwa ya bayyana karfin dangantaka da alakar da ke tsakanin Najeriya da Amurka tare da shirin cigaban wannan alaka da aiki tare da juna.

Jiragen Super Tucano na iya ayyukan leken asiri, sintiri da kuma kiyasta tazara tsakanin sama da kasa yayin kai samame ko farmaki, lamarin da zai karfafa kwarewar dakarun sojin sama wurin yaki da ta'addanci da kuma 'yan bindigan daji.

Najeriya ta siya jiragen ne ta wani shiri na sojin kasashen waje wanda sashen tsaro na Amurka mai suna "Total Package Approach" ya shirya kuna ya hada da siyar da sassan jiragen sama.

PRNigeria ta ruwaito cewa, jimillar siyayyar da aka yi ta kai ta $500 miliyan.

Labari mara dadi: 'Yan fashin daji sun sheke 'yan banga 2 a jihar Niger

A wani labari na daban, sakamakon musayar ruwan wuta tsakanin miyagun 'yan bindigan daji da 'yan banga da aka yi a yankin Mayaki da ke karamar Lapai ta jihar Niger, 'yan banga 2 sun rasa rayukansu.

Kara karanta wannan

Dalla-dalla: Matakai 5 da zaku bi wajen cike fom na shirin 'Nigeria Jubilee Fellows'

Daily Trust ta ruwaito cewa, Mayaki na da iyakoki da Gwaji, wani yanki na karamar hukumar Abaji da ke babban birnin tarayya.

Mazauna yankin sun ce, lamarin ya auku a ranar Lahadi wurin karfe 10:23 na safe yayin da wasu 'yan banga suka fita sintiri kuma miyagun 'yan bindiga suka biyo su a yankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel