An bindige hatsabiban 'yan fashi da suka kitsa kai hari ofishin 'yan sanda da kashe sifeta
- Yan sanda sun kashe wasu hatsabiban yan fashi da makami biyu a jihar Imo
- Yan sandan sun kai samame ne mabuyar Modukpe, suka halaka shi bayan musayar wuta
- Yan sandan sun kuma kashe wani dan tawagar tare da raunata wasu da harsashin bindiga
Imo - 'Yan sanda a Imo sun ce sun bindige wasu hatsabiban 'yan fashi da makami biyu, wadanda su da tawagarsu suka dade suna addabar mutanen garin Obiakpo a karamar hukumar Ohaji na jihar, rahoton Daily Trust.
Sanawar da kakakin yan sandan jihar CSP Mike Abattam ya fitar ta ce yan sandan bayan samun bayannan sirri sun kai samame mabuyar shugaban tawagar suka kashe shugaban, Modestus Ugwuoha wanda aka fi sani da 'Modukpe' da wani guda.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce sauran 'yan tawagar sun tsere da raunin bindiga a jikinsu kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Ya kara da cewa jami'an yan sandan suna bin sahun sauran yan tawagar da suka tsere.
A cewar Abattam, tawagar ce ta kitsa harin da aka kai ofishin yan sanda na Njaba tare da kashe jami'i mai mukamin sufeta.
Sanarwar ta ce:
"A ranar 6 ga watan Satumban 2021, misalin karfe 8 na dare bayan tattaro bayannan sirri, tawagar yan sanda na musamman sun kai samame mabuyar kungiyar yan ta'adda da suka dade suna adabar Obiakpo a karamar hukumar Ohaji Egbema a Jihar Imo.
"Da isar yan sandan, bata garin suka fara harbi, suka yi musayar wuta. Yan sanda sun yi nasara a kansu, an kashe biyu cikin bata garin yayin da saura suka tsere da raunin bindiga, an kuma kwato bindigu a hannunsu."
Sanawar ta cigaba da cewa mutanen garin sun yi murnar jin labarin kashe Modukpe kuma bayanai sun nuna shine ya kitsa harin ofishin yan sanda na Njaba inda aka kashe sufetan yan sanda.
Yan bindiga sun afka ofishin ƴan sandan Zamfara, sunyi kisa, sun sace bindigu AK-47 masu yawa
A wani labarin daban, wasu ɓata gari da ake kyautata zaton ƴan bindiga ne sun kai hari ofishin yan sanda a Zamfara sun kashe jami'in ɗan sanda ɗaya, rahoton SaharaReporters.
Yan bindiga sun kuma kashe wani shugaban ƴan banga da wasu mutane biyu a garuruwan Nahuce da Gidan Janbula a ƙaramar hukumar Bungudu.
Har wa yau, ƴan bindigan sun yi awon gaba da mutane hudu yayin da suka kawo harin.
Asali: Legit.ng