Jeff Bezos Ya Ɗauka Nauyin Binciken Fasahar Da Za Ta Sa Ɗan Adam Ya Rayu Har Abada

Jeff Bezos Ya Ɗauka Nauyin Binciken Fasahar Da Za Ta Sa Ɗan Adam Ya Rayu Har Abada

  • Mai kudin duniya, Jeff Bezos ya dauka nauyin fasahar da za ta sa mutum ya nunka shekaru a kan shekarun da ya kamata ya yi a duniya
  • Kamfanin sa ya dauka kwararrun masana wadanda ake ji da su daga jami’o’i daban-daban suna bincike akan yadda dan Adam ya ke tsufa da yadda za a iya dakatar da tsufar
  • Fasahar za ta sauya yadda kwayar halittar dan Adam ta ke sauya wa sakamakon shekaru ta mayar da ita tamkar ta jinjiri wanda aka haifa babu dadewa kuma ta tsayar da ita a hakan

An samu rahotanni a kan yadda mai kudin duniya, Jeff Bezos ya dauka nauyin fasahar da za ta kara wa rayuwar dan Adam shekaru 50 a kan shekarun da ya debo zai yi a doron duniya.

Kamar yadda LIB suka wallafa, A cewar Bezos wanda daya ne daga cikin biloniyoyin duniyan da suka sanya kudin su a wurin binciken Altos Labs, wata fasahar Silicon Valley ta na aiki a kan hanyoyin kara wa rayuwa tsawo.

Kara karanta wannan

Sunday Igboho ya ce a mika shi ga Najeriya bai jin tsoron karo da gwamnatin Buhari

Jeff bezos ya dauka nauyin binciken fasahar da za ta sa dan Adam ya rayu har abada
Jeff bezos ya dauka nauyin binciken fasahar da za ta sa dan Adam ya rayu har abada. Hoto daga Unknown Facts
Asali: Facebook

Kamfanin da zai yi binciken ya dauka masana kuma kwararru

Sabon kamfanin ya dauki masana masu tarin yawa daga jami’o’i daban-daban don su yi bincike a kan yadda kwayoyin halittar dan Adam suke tsufa da hanyoyin dakatar dasu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wannan fasahar ta musamman za ta dakatar da kwayar halittar dan Adam ne ta mayar da shi tamkar ta jinjiri kuma ta tsayar da su kwayoyin halittar a hakan don kada su cigaba da tsufa, LIB suka ruwaito.

Cikin masanan da aka dauko musamman don wannan binciken akwai Juan Carlos Izpisua Belmonte. Sananne ne shi a harkar hada kwayayen dan Adam da na biri sannan ya gano idan hakan zai sa shekarun dan Adam din da za a samar su karu da shekaru 50.

An fara gwada binciken a kan beraye

Sai dai a lokacin da Belmonte ya gwada binciken sa a kan beraye, sun nuna wasu alamu na kara yarinta maimakon tsufa amma a cikin su akwai wadanda wata cuta mai suna teratomas ta afka wa.

Kara karanta wannan

COVID-19: Gwamna Wike ya fara maganar kakaba sabon takunkumin zaman kulle a gida

Altos Labs suna kokarin ganin sun samar da wata hanyar mayar da tsoho yaro a ko wanne bangare na jiki, amma zai iya daukar shekaru masu yawa kafin a yi amfani dasu ga ‘yan Adam.

Binciken ya yi mutukar birge Bezos wanda hakan yasa ya sanya kudadensa a kai bayan ya taba sanya kudi a kamfanin dakatar da tsufa na Unity Biotechnology.

A cikim wasikar da aka yi wa masu hannayen jari a Amazon, Bezos ya yanko wata maganar wani Richard Dawkins wanda dama bai yi imani da Ubangiji ba inda yake cewa:

“Dakatar da mutuwa abu ne wanda ya kamata a yi aiki a kan shi... idan masu rai basu taru sun dakatar da mutuwa ba, a hankali za ta yi ta musu dauki dai-dai har sai ta karar da kowa.”

Masari: Mafi Yawancin Ƴan Bindiga Fulani Ne Da Ke Cewa Su Musulmi Ne Kaman Ni

A wani labari na daban, Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina ya ce mafi yawancin 'yan bindiga fulani ne kaman shi, ya kara da cewa suna magana harshen Fulfulde kuma suna cewa su musulmi ne, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Nasara: 'Yan bindiga sun gurzu, suna rokon jama'a yafiya tare da sako wadanda suka sace a Zamfara

Ya ce mafi yawancin yan arewa ba su za su yarda da hakan ba amma ya ce zancensa gaskiya ne.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya ke magana a shirin siyasa na 'Politics Today' a gidan talabijin na Channels.

Asali: Legit.ng

Online view pixel