COVID-19: Gwamna Wike ya fara maganar kakaba sabon takunkumin zaman kulle a gida
- Nyesom Wike ya ja-kunnen mutanen Ribas kan kin bin ka’idojin yaki da cutar COVID-19
- Gwamnan yace idan aka cigaba da yi wa dokoki kunnen-kashi, za a kai ga rufe gari
- A cikin ‘yan kwanakin nan, ana ta yawan samun masu dauke da Coronavirus a Ribas
Rivers – Gwamnan Ribas, Nyesom Wike yace gwamnati na iya kai wa dawo da dokar zaman gida idan jama’a ba su bin matakan kare kai daga COVID-19.
Daily Trust ta rahoto cewa Gwamnan jihar Ribas ya bayyana haka ne a lokacin da ‘yan jarida suka yi hira da shi a ranar Litinin, 6 ga watan Satumba, 2021.
Gwamnan ya bayyana haka bayan ganin alkaluman masu kamu wa da cutar COVID-19 da wadanda suka mutu a Ribas kamar yadda NCDC ta fitar.
Mai girma Nyesom Wike yake cewa adadin wadanda cutar ta harba ko ta kashe a makonni biyun da suka wuce suna ta kara yawa saboda rashin bin doka.
Jaridar ta rahoto Wike yana cewa mazauna da masu shigo wa Ribas ba su bin ka’idojin da aka kafa.
Duk da gwamnatin Ribas za ta so jama’a su cigaba da harkokin rayuwa da addinin da ke gabansu, Wike yace za a iya tursasa masu daukar mataki mai tsauri.
“Akwai yiwuwar a tursasa mana, mu dawo da takunkumin COVID-19 da aka dakatar a jihar idan masu dauke da cutar suka cigaba da karu wa fiye da kima.”
Kamar yadda Wike ya bayyana, Ribas tana iya fuskantar matsalar lafiya idan har mutane suka rika rayuwa tamkar babu wannan cuta ta Coronavirus a jihar.
“Karyar banza ce, ba za mu iya cigaba da rufe idanu, mu kawar da kai daga barazanar ba. Rashin yin abin da ya kamata yana da tasiri a lafiya da rayuwar kowa.”
“Ina tuna wa mazauna da dokokin da suke kasa na wanke hannuwa, bada tazara, rufe fuska a bainar jama’a, da yin gwaji da zarar an ji alamun rashin lafiyar.”
A ranar Litinin aka bada sanarwar cewa Dr. Ifedayo Morayo Adetifa ya zama Darekta-Janar na hukumar NCDC. Tolu Ogunlesi ya bayyana haka a shafin Facebook.
Rahoton yace sabon Darektan zai canji Dr. Chikwe Ihekweazu wanda ya tafi kungiyar WHO. Ifedayo Adetifa mataimakin Farfesa ne a wata makaranta a Landan.
Asali: Legit.ng