Ku Gaggauta Nemo Dabarun Magance Matsalar Tsaron Najeriya, Buhari Ya Umarci Hafsoshin Tsaro

Ku Gaggauta Nemo Dabarun Magance Matsalar Tsaron Najeriya, Buhari Ya Umarci Hafsoshin Tsaro

  • Shugaba Buhari ya umarci shugabannin tsaron ƙasar nan su nemo hanyoyi da dabarun magance ƙalubalen tsaro
  • Shugaban ya sabunta wannan umarnin yayin taronsa da shugabannin tsaron yau a fadarsa dake Abuja
  • Ministan Tsaro, Bashir Magashi, yace ragowar jiragen yakin da gwamnati ta siyo daga Amurka zasu iso Najeriya mako mai zuwa

Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya umarci shugabannin tsaro su gaggauta nemo hanyoyin warware ƙalubalen tsaro da ya addabi ƙasar nan, musamman a arewa maso yamma da arewa maso tsakiya.

Channels TV ta rahoto cewa Buhari ya bada wannan umarnin ne a fadarsa dake Abuja, yayin taronsa da shugabannin tsaro, wanda ya shafe awanni biyar ranar Talata.

Shugaban ya jaddada bukatar dakile ayyukan yan bindiga, waɗanda a cewar shugabannin tsaron suna kashe al'umma da sace su domin jawo hankalin duniya.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Gode Mana Bisa Kokarin da Muke Yi, IGP Ya Magantu Bayan Taron Tsaro a Aso Villa

Taron tsaro
Ku Gaggauta Nemo Dabarun Magance Matsalar Tsaron Najeriya, Buhari Ya Umarci Hafsoshin Tsaro Hoto: Buhari Sallau FB Fage
Asali: Facebook

Wane abubuwa aka tattauna a wurin taron?

Ministan tsaro, Janar Bashir Magashi, ya shaidawa manema labaran gidan gwamnati bayan taron cewa gwamnati ta sake nazari kan yanayin da ƙasa ke ciki.

A cewar Magashi taron ya cimma matsaya cewa za'a nemo hanyoyin magance duk wani ƙalubalen tsaro musamman a Zamfara da arewa ta tsakiya, wanda taron ya maida hankali a kai.

Bugu da kari ministan ya bayyana cewa gwamnati zata samu nasarar cimma waɗannan muradan ne idan yan Najeriya sun bata haɗin kai.

Mako mai zuwa sabbin jiragen yaƙi zasu karaso

Magashi ya ƙara da cewa mako mai zuwa rukuni na biyu na jiragen yaƙin A - 29 Super Tucano zasu ƙariso Najeriya, yayin da aka fara gwajin jiragen da suka iso a rukunin farko.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari Ya Shiga Ganawa da Shugabannin Tsaro a Fadarsa Aso Villa

Taron tsaron da ya gudana yau, ya samu jagorancin shugaban ƙasa Buhari, inda baki ɗaya shugabannin tsaro suka halarta.

Hakanan kuma shugabannin tsaron bisa jagorancin shugaban jami'an tsaro, Manjo Janar Lucky Irabor, da ministan tsaro, Janar Bashir Magashi.

Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai sufeto janar na yan sanda, Usman Baba, Ministan Shari'a, Abubakar Malami, ministan cikin gida, Rauf Aregbesola, da ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama.

A wani labarin kuma Fitar da Ɗanyen Mai: Saudiyya Kawar Kirki Ce, Ta Jima Tana Mutunta Najeriya, Buhari

Shugaba Buhari ya gana da ministan harkokin waje na ƙasar Saudiya, Yarima Al-Saud a fadarsa dake Abuja.

Buhari ya yaba da kyakkyawar alaƙar dake tsakanin Najeriya da Saudiya wanda ya samo asali shekaru da dama da suka shuɗe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel