Wadanda ke addabar Najeriya za su fuskanci hukuncin Allah nan ba da jimawa ba - Fitaccen Fasto

Wadanda ke addabar Najeriya za su fuskanci hukuncin Allah nan ba da jimawa ba - Fitaccen Fasto

  • Mugayen mutane da ke addabar zaman lafiya a Najeriya ta hanyar aikata laifuka za su gamu da karshensu cikin kankanin lokaci
  • Wannan shine hasashen Bishop Francis Oke, shugaban kungiyar Pentecostal Fellowship of Nigeria (PFN)
  • Oke ya bayyana cewa irin wadannan mugayen mutane ne da za su hadu da hukuncin Allah sai dai idan sun canza

Shugaban kungiyar Pentecostal Fellowship of Nigeria (PFN) na kasa, Wale Oke, ya ce Allah zai yi maganin wadanda ke addabar Najeriya idan ba su tuba ba.

Oke ya yi wannan tsokaci ne a cikin wata sanarwa da Kayode Oladeji, mai taimaka masa kan harkokin yada labarai ya fitar a ranar Litinin, 7 ga watan Satumba.

Wadanda ke damun Najeriya za su fuskanci hukuncin Allah nan ba da jimawa ba - Fitaccen Fasto
Fitaccen Fasto, Francis Oke ya ce wadanda ke damun Najeriya za su fuskanci hukuncin Allah nan ba da jimawa ba Hoto: PFN
Asali: Facebook

Shugaban na PFN, wanda ke jagorantar cocin Sword of the Spirit Ministries a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, ya ce ayyukan “mugayen mutane” sun jefa kasar cikin mawuyacin hali, PM News ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ba mu da hannu cikin kashe-kashen matafiya a Jos, Matasan Irigwe sun magantu

Oke ya ce:

“Irin wadannan mutane za su fuskanci fushin Allah a cikin yanayin da ba za a iya misalta su ba idan suka ki canza hanyoyin su.
"Akwai mugayen mutane a wannan kasar da Allah zai yi maganin su sai dai idan sun tuba.
"Ayyukan su ya jefa 'yan Najeriya da yawa da kasar cikin mawuyacin hali."

A cewar malamin, duk da nuna ayyukan wadanda ke haddasa wahala a kasar, Najeriya za ta yi nasara.

“Najeriya za ta ci gaba, Najeriya za ta yi nasara.
“Akwai mutanen da ke addabar Najeriya; sai dai idan sun tuba, Allah zai yi maganin su.”

Sheikh Gumi: Tura sojoji su ragargaji 'yan bindiga ba zai magance rashin tsaro ba

A wani labarin, babban malamin addinin Islama mazaunin jihar Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, ya yi ikirarin cewa farmakin da sojoji ke kaiwa kan 'yan bindiga da ke addabar Arewa maso Yamma ba zai magance matsalolin tsaro da kasar ke fuskanta ba.

Kara karanta wannan

NCC: Babu maganar dawo da Twitter yanzu duk Najeriya tayi asarar Naira Biliyan 200

Malam Gumi ya bayyana hakan ne a ranar Litinin 6 ga watan Satumba ta shafinsa na Facebook, yayin da yake mayar da martani kan nasarorin da sojoji ke samu a kan 'yan bindiga a dazuzzukan Zamfara.

Sanarwar, mai taken: ‘Zamfara: The Flaring of Crisis’, ta jaddada cewa matakin soji kan masu aikata miyagun laifuka “ba mafita bane ko hikima”.

Asali: Legit.ng

Online view pixel