NCC: Babu maganar dawo da Twitter yanzu duk Najeriya tayi asarar Naira Biliyan 200

NCC: Babu maganar dawo da Twitter yanzu duk Najeriya tayi asarar Naira Biliyan 200

  • Hukumar NCC tace har zuwa yanzu ba a halasta amfani da Twitter a Najeriya ba
  • Ikechukwu Adinde yace kawo yanzu babu wata takarda daga Ministan sadarwa
  • Rahotanni sun ce haramta amfani da Twitter ya sa ana yin asarar makudan kudi

Abuja- Shugaban sashen hulda da jamaa’a na hukumar NCC, Dr. Ikechukwu Adinde, yace har yanzu haramcin amfani da shafin Twitter yana aiki.

Jaridar Punch ta rahoto Dr. Ikechukwu Adinde yana cewa ma’aikatar sadarwa ba ta yi magana da hukumar NCC a kan a janye wannan dakatarwar ba.

Jami’in hukumar sadarwa na kasar ya yi wannan magana ne kusan watanni uku bayan bada umarni a hana ziyartar shafi da manhajar zamanin.

Sai ma’aikatar sadarwa ta ba hukumar NCC ta kasa umarni, sannan su kuma za su rubuta takarda su bukaci kamfanonin sadarwa su cire takunkumin.

Kara karanta wannan

Ba zan cigaba da lamuntar ta'addanci ba, Lalong ga shugabannin Jos

An yi rashi a Najeriya

Mutane su kan yi amfani da dandalin Twitter wajen tallata hajarsu. Tun da gwamnatin tarayya ta dauki wannan mataki, abubuwa sun tsaya cak a kasar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Statista ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta kashe kimanin Naira biliyan 220.36 domin kamfanonin sadarwa su toshe kafar ziyartar shafin.

Taron FEC
Virtual FEC a Aso Villa Hoto: ait.live
Asali: UGC

Rahoton yace an samu wannan alkaluma ta hanyar lissafin sa’o’in da aka yi ana toshe shafin. Ana biyan $250, 600 a duk sa’a da nufin cin ma manufar.

A kudin gida, gwamnatin Muhammadu Buhari tana kashe Naira miliyan 103.17 domin a haramta Twitter. An dauki da sa’o’i 2, 136 da hana bibiyar Twitter.

Duk da hakan yana ci wa gwamnati Naira miliyan biyu da rabi kullum, har yau ba a cire takunkumin ba, jama'a suna sa ran an kusa sasanta wa.

Kara karanta wannan

Raba-gari: A karshe Shugaba Buhari ya bayyana wadanda ke daukar nauyin IPOB

Haka zalika kamfanin na Twitter yana yin asara saboda rashin kasuwanci a Najeriya. Kamfanin yana samun makudan dalolin kudi daga wajen Amurka.

Tallafin fetur ya ci N540bn

Dazu mu ka ji Gwamnatin Muhammadu Buhari ta na batar da kusan Naira biliyan 2 duk rana a kan tallafin fetur bayan an yi kokarin daina biyan kudin.

Biyan tallafi domin a bar farashin mai a N165 ya jawowa Gwamnati asarar N1.1tr. NNPC ta ce farashin Dala ya sa ‘yan kasuwa suka daina shigo da fetur.

Asali: Legit.ng

Online view pixel