Matsalar Tsaro: Yan Bindiga Sun Sace 'Ya'yan Basarake Guda Hudu a Jihar Katsina
- Wasu miyagun yan bindiga sun yi awon gaba da 'yayan dagacin ƙauyen Sabuwar ƙasa a jihar Katsina
- Harin ya zo awanni 24 kacal bayan wasu mahara sun sace kanwar mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar
- A makonnin nan yan bindiga sun sace ƴaƴa, yan uwa da matan masu rike da mukaman siyasa da dama a Katsina
Katsina - Wasu yan bindiga sun sake kai sabon hari a wani ƙauyen Katsina, inda suka sace ƴaƴan dagacin ƙauyen guda huɗu, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
A cewar wani mazaunin ƙauyen, yan bindiga sun kai hari ƙauyen Sabuwar Ƙasa, karamar hukumar Kafur, da safiyar Litinin, inda suka yi awon gaba da ƴaƴan Alhaji Hamza Umar.
Umar, wanda shine dagacin ƙauyen Sabuwar ƙasa, yana jagorantar majalisar gudanarwa ta ƙaramar hukumar Funtua, a jihar Katsina.
Bayan Datse Sabis a Zamfara, Gwamnatin Tarayya Ta Yi Magana Kan Datse Sabis Na Sadarwa a Jihar Katsina
Sai dai har zuwa yanzun rundunar yan sanda reshen jihar ta Katsina ba ta ce komai ba game da sace yaran dagacin, kamar yadda premium times ta ruwaito.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ɓarayi sun sace yar uwar mataimakin kakakin majalisa
Awanni 24 kafin faruwar wannan lamarin, wasu yan bindiga suka sace kanwar mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Katsina, Shehu Ɗalhatu Tafoki.
Hakazalika kafin wannan, wasu ɓarayi sun kai hari ƙauyen Kurami, karamar hukumar Bakori dake jihar Katsina ranar Asabar.
Yayin harin ɓarayin sun yi awon gaba da mata da ƴaƴa biyu na ɗan majalisa mai wakiltar Bakori a majalisar dokoki, Dakta Ibrahim Kurami.
Bakori na da nisan kilomita 42 zuwa ƙaramar hukumar Faskari, wacce take cikin yankunan da hare-hare suka fi kamari a jihar.
Wane hali jihar Katsina take ciki?
A cikin yan makonnin nan da suka shuɗe, jihar Katsina na fuskantar jerin hare-haren yan bindiga.
Ba Inda Zanje, Nima Zan Ɗanɗani Duk Wahalar da Jama'ata Ke Ciki, Matawalle Ya Soke Duk Wani Fita Zamfara
Maharan sun maida hankali kan sace ƴaƴa, ƴan uwa da kuma matan yan majalisun dokokin jihar da masu rike da mukaman siyasa.
A wani labarin kuma Gwamnan Zamfara ya soke duk wasu tafiye-tafiye da zasu fitar da shi jihar Zamfara bayan datse sabis
Gwamnan yace ba inda zaije duk halin da al'ummar jihar Zamfara suka tsincin kan su a dai dai wannan lokacin to da shi za'a sha wahalar.
A makon da ya gabata ne hukumar sadarwa NCC ta umarci baki ɗaya kamfanonin sadarwa su datse sabis ɗinsu a jihar Zamfara.
Asali: Legit.ng