Jami'ar Nigeria ta dakatar da farfesan da ake zargi da ƙaryar rage shekarunsa
- Jami'ar Koyar Aikin Noma na Tarayya da ke Abeokuta (FUNAAB) ta dakatar da Farfesa AbdulAkeem Agboola
- Kakakin Jami'ar FUNAAB, Kola Adepoju, ya ce an dakatar da farfesan ne don zurfafa bincike kan shekarunsa da takardun karatunsa
- Adepoju ya ce jami'ar ta fara zargin akwai matsala ne bayan ya yi bikin ciki shekaru 60 a gari amma a takardan makarantar shekarunsa 56
Mahukunta a Jami'ar Koyar Aikin Noma na Tarayya da ke Abeokuta (FUNAAB) ta dakatar da wani malami a jami'ar, AbdulAkeem Agboola, kan zarginsa da karya a shekarunsa da sunansa a takardun da ya mika wa jami'ar.
Kola Adepoju, mai magana da yawun jami'ar ya shaidawa Premium Times a ranar Litinin cewa an kafa kwamiti domin bincike sosai kan lamarin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mr Adepoju ya ce:
"A matsayin mu na jami'a, muna da tsari a jami'ar ta yadda muke duba irin wannan matsalar, na farko shine kafa kwamiti da za ta duba lamarin kuma an yi hakan."
"Kwamitin ta bukaci a dakatar da shi don haka a yanzu da muke magana an dakatar da shi. Wannan ba shine karshe ba domin ana cigaba da bincike kuma za mu sanar da ku yadda abin ke tafiya."
Premium Times ta tattaro cewa Mr Agboola ya yi bikin cika shekaru 58 a 2018, sannan bikin cika shekaru 60 a bara; takardar shekarar haihuwarsa da ya bawa makarantar ya nuna cewa an haife shi a 1956, ma'ana shekarunsa 56 a 2021.
Wasu majiyoyi a jami'ar sun bayyana cewa mahukunta FUNAAB sun fara bincike kansa ne bayan sun gano ya yi bikin ciki shekaru 60 a bara.
Shugaban APC na kasa: Jigon jam’iyyar ya ce Ali Modu Sheriff ya cancanci jagorantar jam’iyyar mai mulki
Bayan hakan ne makarantar da rubuta wa Mr Agboola wasika a ranar 13 ga watan Afrilu tana bukatar ya tura maka takardun shaidan haihuwarsa da takardan digirinsa na biyu da na uku.
An bukaci ya mika takardun kafin ko ranar 16 ga watan Afrilun 2021.
Abin da Farfesa Agboola ya ce game da batun?
A bangarensa, Mr Agboola ya ce wasikar da jami'ar ta rubuta masa wasika tare da cew bai mika wa makarantar takardunsa na M.Sc da Ph.D ba abin kunya ne da damuwa.
Ya ce sau biyu ana bincikarsa a makarantar kuma ya nuna takardunsa na ainihi da fotokopi.
"Ina fatan ba wani ne ke neman yin wasa da takardu na ba a ofishin ajiye takardu," in ji Agboola.
Har cikin silin na ke ɓoye kuɗi amma tana shiga ta sace: Miji ya nemi a raba aure don satar da matarsa ke masa
A wani labarin daban, wata kotun gargajiya mai zamanta a Igando a jihar Legas, a ranar Alhamis ta tsinke auren mata da miji da suka shafe shekaru 10 suna zaman aure saboda halin sata da matar ke da shi, Premium Times ta ruwaito.
Mutiu Bamgbose, dan kasuwa mai shekaru 45, ya kuma zargi matarsa Aliyah da cin amanarsa na aure.
Da ya ke yanke hukunci, alkalin kotun, Adeniy Koledoye, ya ce babu tantama auren na su ba mai gyaruwa bane duba da cewa wacce aka yi karar ta ta ki amsa gayyatar kotun, Daily Nigerian ta ruwaito.
Asali: Legit.ng