Da Ɗumi-Ɗumi: An Kashe Mutane 3 a Sabon Harin Da Aka Kai a Plateau

Da Ɗumi-Ɗumi: An Kashe Mutane 3 a Sabon Harin Da Aka Kai a Plateau

  • An sake kashe mutane uku a jihar karamar hukumar Bass ta jihar Plateau
  • Fulani makiyaya da kuma 'yan kabilar Irigwe duk sun ce ba su da hannu a kisar
  • A baya-bayan nan ne dai bangarorin biyu suka ratabba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya

Plateau - An halaka mutane uku a ƙauyuka biyu da ke ƙaramar hukumar Bassa ta jihar Plateau a sabbin hare-haren da aka kai kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Daily Trust ta ruwaito cewa an kai hare-haren biyu ne mabanbanta a ƙauyuka biyu.

Da Ɗumi-Ɗumi: An Kashe Mutane 3 a Sabon Harin Da Aka Kai a Plateau
Da Ɗumi-Ɗumi: An Kashe Mutane 3 a Sabon Harin Da Aka Kai a Plateau
Asali: Original

Kara karanta wannan

Bamu yi sulhu da Fulani ba: Yan Irigwe da akewa zargin kashe matafiya a Jos

Harin na farko ya faru ne a ranar Lahadi da yamma a garin Kwachudu inda aka kashe wani makiyayi.

Miyetti Allah ta ce bata da hannu a harin

Shugaban kungiyar Makiyaya na Miyetti Allah, MACBAN, na jihar, Malam Nura Abdullahi ya zargi yan kabilar Irigwe da datse kan wani Musa Sale yayin da suka raunata Abdulsalam Nuhu yayin da suke kiwon dabbobi a Kwachudu.

Yan Kabilar Irigwe sun ce ba su da hannu a harin

Yan kabilar Irigwe sun musanta zargin, suna mai cewa ba gaskiya bane kuma babu wani hujja da ke nuna su suka aikata kisar.

Awanni bayan garin na yammacin Lahadi, an kashe yan kabilar Irigwe biyu a safiyar ranar Litinin a garin Renwienku a ƙaramar hukumar Bassa.

Malison David, ƙalla kungiyar yan Irigwe, IDA, ya zargi Fulani da kai harin amma kungiyar Fulani sun musunta zargin.

Harin na zuwa ne kwanaki biyar bayan kabilun biyu sun yi taron zaman lafiya da gwamnan jihar Simon Lalong sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Shugaban APC na kasa: Jigon jam’iyyar ya ce Ali Modu Sheriff ya cancanci jagorantar jam’iyyar mai mulki

Kakakin yan sanda na jihar, ASP Ubah Gabriel bai ɗaga wayarsa ba kuma bai amsa sakon kar ta kwana da aka aika masa ba.

Kashe-Kashen Jos: CAN ta miƙa muhimman saƙo ga shugabannin musulmi da kirista a Plateau

A wani labarin daban, Kungiyar kirista ta Nigeria, CAN, a Jos, babban birnin jihar Plateau ta roki shugabannin musulmi da na kirista su dena tunzura mutane suna miyagun ayyuka, Peoples Gazette ta ruwaito.

A cewar sanarwar da ta fitar a garin Jos a ranar Laraba mai dauke da sa hannun shugaban CAN, Polycarp Gana da satare Ezekiel Noam, kungiyar ta kuma yi Allah wadai da kashe-kashen da aka yi a Yalwan Zangam.

Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun afka garin a daren ranar Talata sun kashe mutane masu yawa sannan suka kona gidaje da dama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel