Ka Taimaka Ka Bada Umarnin Turo Dakarun Sojoji Yankin Masarautata, Sarki Ya Roki Shugaba Buhari

Ka Taimaka Ka Bada Umarnin Turo Dakarun Sojoji Yankin Masarautata, Sarki Ya Roki Shugaba Buhari

  • Sarkin Borgu, Muhammad Dantoro, ya roki shugaba Buhari ya bada umarnin a tura dakarun sojoji yankin masarautar Borgu
  • Wannan kiran na zuwa ne bayan wasu yan bindiga sun sace basaraken Wawa dake yankin masarautar Burgu
  • Sarkin ya kuma bayyana cewa yana nan cikin koshin lafiya kuma rahoton dake cewa an sace shi ba gaskiya bane

Niger - Sarkin Borgu, jihar Neja, Muhammad Dantoro, ya yi kira ga shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya taimaka ya bada umarnin a turo sojoji yankin Borgu domin magance masu garkuwa, kamar yadda punch ta ruwaito.

Da yake martani kan sace Basaraken Wawa, Dakta Mahmud Ahmed, wanda aka yi a Borgu, Sarkin yace ya zama wajibi akansa ya yi wannan kiran ga shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi awon gaba da yayan Sakataren Gwamnatin jihar Katsina

Shugaba Buhari da sarkin Burgu
Ka Taimaka Ka Bada Umarnin Turo Dakarun Sojoji Yankin Masarautata, Sarki Ya Roki Shugaba Buhari Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Sarkin yace:

"Wannan kiran na gaggawa ne, muna bukatar gwamnati ta gaggauta turo mana dakarun sojojin ƙasa da na sama domin su binciko mana yan tada kayar baya."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sarki ya musanta rahoton sace shi

Basaraken ya musanta raɗe-raɗen cewa yan bindiga sun sace shi, inda ya kara da cewa yana nan cikin koshin lafiya.

"Mutane na kusa da na nesa sun kira ni ta wayar salula, suna son tabbatar da lafiya ta. Eh ina lafiya, ba ni maharan suka sace ba, hakimin Wawa aka ɗauke kuma a karkashin masarautata yake."
"Hakanan kuma, an sace basaraken Dekara watanni huɗu da suka gabata kuma har yanzun ba'a gano shi ba."
"Bana jin daɗin abinda ke faruwa a yankina, kuma ina rokon a turo sojoji su shiga dajin Kainji domin su kuɓutar da basaraken da sauran mutanen da yan bindiga ke tsare da su."

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya yi Allah wadai da hallaka dan Sanata Bala Na'Allah da aka yi

Sarkin Borgu yace ya kamata a gaggauta ɗaukar mataki tun kafin maharan su fice daga dajin zuwa jamhuriyar Benin.

Sojoji sun yi luguden wuta kan yan bindiga

A wani labarin kuma Bayan Datse Sabis, Jiragen Yakin Sojoji Sun Yi Luguden Wuta Kan Sansanonin Yan Bindiga a Zamfara

Kwanaki ƙalilan bayan gwamnatin Zamfara ta sanar da ɗaukar wasu matakai domin magance ayyukan yan bindiga, sojojin sama da na ƙasa sun yi luguden wuta kan yan bindiga a sansanonin su.

Jiragen yakin sama na sojoji ne suka fara ruwan wuta kan yan tada kayar bayan daga bisani sojin ƙasa suka buɗe wuta kan masu tserewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: