Sheikh Ahmad Gumi ya je garin Fulani don wa'azi da raba musu littafan addini

Sheikh Ahmad Gumi ya je garin Fulani don wa'azi da raba musu littafan addini

  • Dr Ahmad Gumi ya kai ziyarar wa'azi Ilori, babbar birnin jihar Kwara
  • Babban Malamin zai gina gidauniya ta musamman a garin ta Ilesha
  • Ya yi addu'an Allah ya karbi wannan aiki ya karesu da dukkan abin ki

Babban Malamin addini, Sheikh Ahmad Gumi, ya kai ziyarar wa'azi Ilori, babbar birnin jihar Kwara domin ganawa da al'ummar Fulani da kuma gina gidauniya ta musamman.

Malam Gumi dai ya shahara da shiga cikin daji don ganawa da Fulani inda yake musu wa'azi kuma kuma gina musu makarantu da rijiyar burtsatsai.

Bisa jawabin da Hadiminsa Salisu Hassan Webmaster ya saki a shafin Facebook, wannan karo, Malamin ya tafi garin Ilesha domin rabawa al'ummar Fulanin littatafan addini.

Ya saki jawabin ne ranar Asabar, 4 ga watan Satumba, 2021.

Kara karanta wannan

Shugaban APC na kasa: Jigon jam’iyyar ya ce Ali Modu Sheriff ya cancanci jagorantar jam’iyyar mai mulki

Yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Sheikh Dr Ahmad Abubakar Mahmud Gumi tare da tawagarsa a garin illesha, Illorin jihar Kwara.
Muna sa ran Malam zai gana da Al'ummar Musulmai Fulani mazauna wani kauye tare da yi musu nasiha da kuma raba musu littafan addini da daura ginshikin gina musu mu'assah ta Sheikh Usman bn Fodio Foundation.
Cikin tawagarsa akwai Sheikh Sunusi Kutama, Sheikh Muhammad Adam Sulaiman, Farfesa Usman Yusuf da Mal. Murtala Abdullahi"

Sheikh Gumi ya je garin Fulani don wa'azi da raba musu littafan addini
Sheikh Ahmad Gumi ya je garin Fulani don wa'azi da raba musu littafan addini Hoto: Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Asali: Facebook

Yan siyasa duk suka lalata Malaman addini, shi yasa basu iya fadin gaskiya: Sheikh Gumi

Sheikh Dr. Ahmad Abubakar Gumi ya yi Alla-wadai da yadda yan siyasa sukayi tururuwa zuwa daurin auren 'dan Buhari da Zahra Bayero.

Babban Malamin ya yi Alla-wadai kan yadda yan siyasa suka yi amfani da dukiyar al'umma wajen baja koli da hayar jiragen alfarma.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi awon gaba da yayan Sakataren Gwamnatin jihar Katsina

Malamin ya yi bayyana dalilin da yasa Malamai ba sa iya fadawa shugabanni gaskiya.

Yace duk yan siyasa sun lalata Malaman addini shiyasa basu iya musu wa'azi, su fada musu gaskiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel