Yan siyasa duk suka lalata Malaman addini, shi yasa basu iya fadin gaskiya: Sheikh Gumi
- Sheikh Ahmad Gumi ya ce a daina ganin laifin Malamai, yan siyasa suka lalatasu
- Babban Malamin yace wani malamin ba zai kwana gidansa ba idan yayi wani magana
- Malam Gumi ya kasance mai rajin ganin karshen matsalar yan bindiga
Kaduna - Shehin Malamin addinin Islam, Sheikh Dr. Ahmad Abubakar Gumi ya yi Alla-wadai da yadda yan siyasa sukayi tururuwa zuwa daurin auren 'dan Buhari da Zahra Bayero.
Babban Malamin ya yi Alla-wadai kan yadda yan siyasa suka yi amfani da dukiyar al'umma wajen baja koli da hayar jiragen alfarma.
Malamin ya yi bayyana dalilin da yasa Malamai ba sa iya fadawa shugabanni gaskiya.
Yace duk yan siyasa sun lalata Malaman addini shiyasa basu iya musu wa'azi, su fada musu gaskiya.
Gumi ya bayyana hakan yayin karatun Tafisrin mako-mako da yake gudanarwa a Masallacin Sultan Bello dake jihar Kaduna.
Yace:
"Kar ku ba Malamai laifi, domin wani Malamin ba zai iya rayuwa sai yayi dan amshin shata saboda yunwa. Wani Malami in yayi wata magana ba zai kwana gidansa ba, cikinCell zai kwana. In kuma an nemeshi zaku je ku fito da shi? Dole yayi shiru."
"Shiyasa Yan siyasa suka lalata mana Malamai. ana barna cikin kasa ba mai wa'azi, ba mai gaya musu gaskiya. Sannan barnan nan babu inda za ta kaimu sai ga wahala."
"Ga kuna barnar kudi jirgae kuke dauka zuwa aure, sannan ga wasu mabarnata a daji suka tatse mutane."
Mutane sun tsamannin wadanda ke daji ke tastanmu, har shugabanninmu suna tatsanmu
Auren dan Shugaba Buhari: Talakan Najeriya ya shiga uku
Sheikh Ahmad Gumi ya yi raddi a kan bikinkan yadda jami'an gwamnati suka kashe kudi domin halartan wannan biki a jihar Kano, inda ya bayyana hakan a matsayin almubazaranci da dukiyar kasa.
Gumi ya ce talakan kasar nan ya shiga uku sai dai ceton Allah kawai, sannan ya shawarci talakawa da su koma ga Allah da gaskiya domin ya cece su.
Kalli bidiyon:
Asali: Legit.ng