Makiyaya sun daura hotunansu a shafin Facebook din wata mata bayan sun sace mata waya, da dama sun yi martani

Makiyaya sun daura hotunansu a shafin Facebook din wata mata bayan sun sace mata waya, da dama sun yi martani

  • An sace wayar wata ‘yar Najeriya mai suna Debora Mbi, inda a halin yanzu shafinta na Facebook ke dauke da hotunan wadanda ake zargin sun sace ta
  • Wasu da ake zargin makiyaya ne sun sace wayar Mbi tare da sanya hotunansu a shafinta na sada zumunta ba tare da tunanin illar abin da suka aikata ba
  • A daya daga cikin hotunan wadanda ake zargin makiyayan sun loda a yanar gizo, ana iya ganin wani mutum tare da garken shanu

Wasu da ake zargin makiyaya ne sun sace wayar wata 'yar Najeriya sannan suka shiga shafinta na Facebook don sanya hotunansu a kai.

Legit.ng ta tambayi masu amfani da Facebook ra’ayinsu game da abun da makiyayan suka yi.

Kara karanta wannan

Yan fashi sun sace Tirelan Dangote dauke da buhuhunan Siminti 900

Makiyaya sun daura hotunansu a shafin Facebook din wata mata bayan sun sace mata waya, da dama sun yi martani
Makiyaya sun daura hotunansu a shafin Facebook din wata mata bayan sun sace mata waya, da dama sun yi martani Hoto: Debora Mbi
Asali: Facebook

Da take wallafa hotunan Debora Mbi da na makiyayan da ake zargi akan Facebook, Legit.ng ta rubuta:

"Wasu da ake zargin makiyaya ne sun loda hotunansu a shafin Facebook din wata mata bayan sun sace wayarta. Yaya zaku bayyana wannan karfin hali nasu?"

Yan Najeriya sun yi martani

Ogochukwu Juliet ya ce:

"Saboda suna da tabbacin za su kwana lafiya. Bari ya kasance daga wani yanki ne, za a saki bataliya guda da ke neman su. A halin yanzu, ba su da hankali."

Ejyke Hillz yayi sharhi:

"Sun jahilci ayyukan su ... shi yasa Ilimi yake da kyau ..."

Sam Ade ya rubuta:

"Wannan na iya faruwa ne kawai a cikin ƙasar da komai baya aiki. Binciken sirri ya gaza. Bin diddigin wayoyin sata ma ya gaza."

Kara karanta wannan

Tubabbun 'yan bindiga sun koma ruwa, sun shiga hannun 'yan sanda a Katsina

Mercy Eberechukwu Promise ta ce:

"Ba abin mamaki bane. Fulani Makiyaya sune manyan 'yan kasa na farko a kasar nan. Mu da muka rage yan baya ne."

A wani labari na daban, yan bindiga masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da Kabir Muhammad Burkai, yaya ga Sakataren gwamnatin Katsina, Alhaji Mustapha Muhammad Inuwa.

Katsina Post ta ruwaito cewa yan bindigan sun saceshi ne ranar Laraba, 1 ga Satumba, 2021 a gonar sa dake wani kauye mai suna Daftau da rana, karamar hukumar DanMusa ta jihar.

Kabir Muhammad Burkai dai mahaifin su daya da Mustapha Inuwa sai dai ba mahaifiyar su daya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng