Kungiya ta yi kira ga Buhari ya tsige wasu Ministoci 2 da Hadiminsa bayan su Sabo Nanono

Kungiya ta yi kira ga Buhari ya tsige wasu Ministoci 2 da Hadiminsa bayan su Sabo Nanono

  • Wasu sun yaba wa shugaban kasa da ya kori wasu daga cikin Ministocinsa
  • Kingsley Moghalu da Sam Amadi sun ji dadin tsige Ministocin 2 da aka yi
  • Kungiyar HURIWA ta bada shawarar a kara da wasu Ministocin, a sallama

Guardian tace ana tofa albarkacin baki bayan samun labarin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kori Ministocinsa; Saleh Mamman da Sabo Nanono.

Jam’iyyar hamayya ta PDP ta bakin Kola Ologbondiyan, cewa tayi shugaban kasar yana kokarin rufe gazawarsa ne da dabarar sallamar Ministocin biyu.

Amma makara a haka - Kingsley Moghalu

Farfesa Kingsley Moghalu wanda ya taba rike kujerar mataimakin gwamnan CBN yace shugaban Najeriyan ya yi daidai da ya sallami wadannan Ministoci.

Kingsley Moghalu ya na ganin an yi jinkiri wajen korar Injiniya Saleh Mamman da Alhaji Sabo Nanono. Jaridar ta fitar da wannan rahoto a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Jam'iyyar APC ta sallami shugabanta da ya ce Buhari ya mutu kowa ya huta

Ya kamata a hada da wasu Ministocin - HURIWA

Kungiyar HURIWA ta masu kare hakkin Bil Adama ta kuma roki Mai girma Muhammadu Buhari ya tsige Abubakar Malami SAN da Janar Bashir Magashi.

Haka zalika kungiyar ta bukaci Buhari ya kori Babagana Monguno daga kujerar NSA. HURIWA ta ce wadannan mutane uku sun gaza tabuka wani abin kirki.

Shugaban HURIWA na kasa, Emmanuel Onwubiko, yace tun ba yau ba, ya kamata a ce an sallami Nanono da Mamman, a cewarsu ba su iya yin komai a ofis ba.

Wasu Ministoci
Saleh Mamman da Sabo Nanono Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

HURIWA ta zargi Ministocin da tabarbarewar samun wutar lantarki da tsadar kayan abinci a Najeriya.

Ganin yadda ake fama da matsalar tsaro da kuma tsare Nnamdi Kanu, Onwubiko ya nemi a sauke Malami da Magashi daga kujerun Ministocin shari’a da tsaro.

Kara karanta wannan

Dakarun Sojin Najeriya sun ragargaji yan ta'addan ISWAP a Borno, sun kashe 6

Har ila yau, tsohon shugaban kungiyar CAFFAN ta manoman tarwada, Rotimi Oloye, ya yi farin ciki da aka yi waje da Nanono, yace a nemi 'dan matashi a nada.

Irinsu tsohon shugaban NERc na kasa, Sam Amadi ya yabi matakin da aka dauka na sauke Saleh Mamman, ya shaida wa Guardian cewa an yi abin da ya kamata.

Meyasa Ministocin suka rasa kujerunsu

A ranar Alhamis ne kuka ji wasu cikin dalilan da ya sa aka yi canji a FEC. An ji Saleh Mamman ya yi fada da shugabannin TCN, REA, NBET da NERC bayan shiga ofis.

Sabo Nanono ya yi ta yin abubuwan da suka jawo masa fushin Shugaban kasa Muhammadu Buhari. A karshe aka bukaci su tattara su sauke daga mukaman na su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel