Kotu ta bada umurnin a tsare 'dodo' saboda zargin kisa bayan kai hari masallaci

Kotu ta bada umurnin a tsare 'dodo' saboda zargin kisa bayan kai hari masallaci

  • Kotun majistare da ke zamanta a Osogbo babban birnin jihar Osun ta umurci yan sanda su tsare mata wani dodo
  • Kotun ta bada umurnin a tsare dodon ne saboda zarginsa da ake yi da hannu wurin kashe wani yayin harin da suka kai masallaci
  • Kotun har ila yau ta bada umurnin a tsare mata limamin masallacin da dodon ya kai hari wasu mabiyansa hudu da ake zargi da dukkan dodon

Wata kotun majistare da ke Osogbo, jihar Osun ta bada umurnin a tsare mata Fashola Esuleke, dodon da ke da hannu cikin fadar da ta yi sanadin rasuwar Alhaji Moshood Salahudeen a masallacin Kamorudeen a babban birnin jihar.

Daily Trust ta ruwaito cewa an tsare Esuleke ne tare da Kazeem Yunus, babban limamin masallacin da huɗu daga cikin mabiyansa.

Kotu ta bada umurnin a tsare 'dodo' saboda zargin kisa bayan kai hari masallaci
Kotu ta bada umurnin a tsare 'dodo' saboda kai hari masallaci.Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Hotunan mataimakin kwamishinan Ƴan Sanda na bogi da aka kama cikin otel a Kano

An gurfanar da limanin ne saboda dukan dodon yayin da an gurfanar da dodon bisa zargin kisa.

Lauyan jihar daga ma'aikatar Shari'a, Moses Faremi, ya shaidawa kotu cewa ma'aikatar na son ƴan sanda ta bari ta cigaba da shari'ar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Lauyan limamin, Qazeem Odedeji, ya shaidawa kotu cewa bai dace a gwamutsa zargin da aka yi wa dodon da limanin a cikin ƙara guda ba yana mai nema a raba su.

KU KARANTA: Kano: Ɗalibi ya cinnawa kansa wuta saboda bai samu kuɗin biyan jarrabawar NECO ba

Alkalin kotun, Asimiyu Adebayo ya amince da bukatar lauyan inda ya umurci rundunar yan sanda ta banbanta ƙarar daga zargin kisar da ake yi wa dodon.

Alkalin kotun ya bada umurnin a tsare masa dukkan wadanda ake zargin a hannun ƴan sanda har zuwa ranar 12 ga watan Yuli don cigaba da shari'ar.

Kaduna: Yaya ya yi ƙarar ƙaninsa a kotun Shari'a saboda ƙin biyayya ga wasiyyar mahaifinsu da ya rasu

A wani labarin, kun ji wani mutum mai shekaru 40, Sani Abubakar, a ranar Alhamis, ya yi ƙarar ƙaninsa Adda'u Ahmed gaban kotun Shari'a da ke zamanta a Rigasa, kan zargin ƙin ƙiyayya ga wasiyyar mahaifinsu, Vanguard ta ruwaito.

Abubakar, wanda ke zaune a unguwar Rigasa a Kaduna ya kuma yi ƙarar wani Malam Shuaibu.

Ya shaidawa kotu cewa mahaifinsu da Allah ya yi wa rasuwa ya bar wasiyya cewa a mayar da ɗaya daga ɗakunan gidan zuwa masallaci amma wadanda ya yi ƙarar sun saɓa umurnin mahaifin a cewar rahoton na Vanguard.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel