Masu garkuwa da mutane sun bindige DPOn 'yan sanda a jihar Edo

Masu garkuwa da mutane sun bindige DPOn 'yan sanda a jihar Edo

  • Wasu bata gari da ake zargi masu garkuwa da mutane ne sun harbi DPOn yan sanda a jihar Edo
  • Bata garin sun harbi dan sandan ne a kan hanyarsa na zuwa Auchi bayan ya baro Igarra
  • Kakakin yan sandan jihar Edo Kontongs Bello ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce dan sandan yana karbar magani

Jihar Edo - Wasu 'yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun harbi DPO na Igarra a karamar hukumar Akoko-Edo, Suleiman Mohammed, The Cable ta ruwaito.

Mai magana da yawun yan sandan jihar Edo, Kontongs Bello, ya tabbatar da hakan a ranar Laraba.

Masu garkuwa da mutane sun bindige DPOn 'yan sanda a jihar Edo
Jami'an 'yan sandan Nigeria. Hoto: The Nation
Asali: Depositphotos

Ta yaya lamarin ya faru?

DPOn yana kan hanyarsa ne daga Igarra zuwa Auchi a lokacin da maharan suka tare shi a hanyar Auchi-Igarra-Ibillo kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tubabbun 'yan bindiga sun koma ruwa, sun shiga hannun 'yan sanda a Katsina

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kontongs Bello ya ce kawo yanzu ba a tabbatar ko harbin da aka yi, a ranar Talatan, wani yunkuri ne na sace jami'in dan sandan.

Dan sandan a halin yanzu yana asibiti yana karbar magani.

Mai magana da yawun yan sandan ya ce;

"Ba a tabbatar ba ko masu garkuwa da mutane ne."
"An harbe shi ne a hanyarsa daga Igarra zuwa Auchi. Tuni an garzaya da shi asibiti yana samun kulawa. Yana samun sauki."

Wannan yana zuwa ne kwanaki kadan bayan yan bindiga sun sace wani likita mai suna Tonnie Okeye a jihar Edo.

An ruwaito cewa Okoye yana tafiya ne a Auchi, karamar hukumar Estako West, aka sace shi a kan babban hanyar Benin zuwa Asaba a karshen mako.

Wani dan uwan likitan ya shaida wa The Cable cewa:

Kara karanta wannan

Shekaru 35 yana aikin koyarwa a Borno, dan Najeriyan da Turawa suka horar ya koma talla

"An sace Dr Tonnie Okoye a kan hanyar Benin zuwa Asaba da rana (Asabar) kuma bata garin suna neman Naira miliyan 100 kafin su sako shi."

Alhaki: Ƴan bindiga 9 sun mutu sakamakon rikici da ya ɓarke tsakanin ɓangarori biyu da basu ga maciji a Kaduna

A wani labarin daban, kun ji cewa kungiyoyi biyu na wasu shu’uman ‘yan bindiga a karamar hukumar Giwa da ke jihar Kaduna inda harbe-harbe ya barke tsakaninsu kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Rikicin ya yi sanadiyyar halakar mutane 9 a cikinsu kamar yadda jami’an binciken sirri suka tabbatarwa da gwamnatin jihar Kaduna.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya sanar da hakan a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel