Zamu kama wadanda suka kai hari NDA komin daren dadewa, Shugaban Hafsin Soji

Zamu kama wadanda suka kai hari NDA komin daren dadewa, Shugaban Hafsin Soji

  • Hukumar Sojin Najeriya tace ko ta kaka sai ta damke wadanda suka kai hari makarantar Sojoji NDA
  • Shugaban Hafsin Sojin, Laftanan Janar Faruk Yahya, yace komin dadewa sai an kamosu
  • Mako guda yanzu ba'a san halin da Manjon da suka sace ke ciki ba

Kaduna - Shugaban Hafsin Sojin kasa Laftanan Janar Faruk Yahaya, ya lashi takobin cewa wadanda suka kai hari makarantar Sojojin Najeriya NDA zasu shiga hannu komin daren dadewa.

Wannan na kunshe cikin jawabin da Kakakin makarantar Soji NDA, Bashir Jajira, ya saki ranar Laraba, 1 ga Satumba, kuma Legit ta gani.

An saki jawabin bayan ziyarar da Babban hafsin Sojin ya kai makarantar ranar Talata, 31 ga Agusta, 2021 domin duba makarantar biyo bayan abinda ya faru.

Kara karanta wannan

Dakarun Sojin Najeriya sun ragargaji yan ta'addan ISWAP a Borno, sun kashe 6

Wani sashen jawabin yace:

"COAS ya lashi takobin cewa komin daren dadewa, wadanda suka aikata wannan abin kunyan zasu shiga hannu."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wannan harin ya janyo cece-kuce inda yan Najeriya sukace abu ya munana tunda har Sojoji basu tsira ba.

Zamu kama wadanda suka kai hari NDA komin daren dadewa, Shugaban Hafsin Soji
Zamu kama wadanda suka kai hari NDA komin daren dadewa Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: UGC

Yaushe yan bindiga suka kai hari NDA?

A ranar 24 ga Agusta, wasu tsagerun yan bindiga sun kai mumunan hari makarantar horar da Sojin Najeriya NDA dake jihar Kaduna.

Yan bindiga sun hallaka Sojoji biyu kuma sukayi garkuwa da guda daya.

Legit Hausa ta tattara muku abubuwa 5 da ya kamata ku sani

Latsa nan don karantasu: https://hausa.legit.ng/1431031-abubuwa-6-da-ya-kamata-ka-sani-game-da-harin-da-yan-bindiga-suka-kai-nda.html

Yan bindigan da suka kai hari NDA sun bukaci N200m kudin fansa

Yan bindigan da suka kai hari makarantar horar da Sojojin Najeriya NDA dake garin Afaka a jihar Kaduna kuma sukayi awon gaba da jami'in Soja sun kira gidan Soja.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun fasa coci, sun yi awon gaba da masu ibada

Sojan da akayi awon gaba da shi sunansa, Manjo Dantong.

A cewar FIJ, yan bindigan sun kira NDA domin tattauna maganar kudin fansa kafin su sake shi.

Sun bukaci a basu kudi N200m idan har ana son Manjon ya dawo da ransa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel