Yan bindigan da suka kai hari NDA sun bukaci N200m kudin fansa

Yan bindigan da suka kai hari NDA sun bukaci N200m kudin fansa

  • Yan bindigan da suka kai hari NDA sun bukaci kudin fansa
  • Yayinda suka kashe Sojoji biyu, ko mutum daya ba'a kashe cikinsu ba
  • Wannan abu ya janyo suka iri-iri ga hukumar Sojoji

Kaduna - Yan bindigan da suka kai hari makarantar horar da Sojojin Najeriya NDA dake garin Afaka a jihar Kaduna kuma sukayi awon gaba da jami'in Soja sun kira gidan Soja.

Sojan da akayi awon gaba da shi sunansa, Manjo Dantong.

A cewar FIJ, yan bindigan sun kira NDA domin tattauna maganar kudin fansa kafin su sake shi.

Sun bukaci a basu kudi N200m idan har ana son Manjon ya dawo da ransa.

Wata majiyar FIJ ta bayyana cewa:

"Ko mutum daya sun kasa kashewa. Sun duba ko ina cikin daji amma basu gansu ba. Sun gudu kan baburansu."

Kara karanta wannan

Bayan sama da watanni biyu, daliban Tegina 6 sun mutu hannun yan bindiga

"Sun kira kuma sun bukaci kudin fansa N200m don sake Manjon. Wannan harin abin takaici ne. Sun shigo, sun mamaye mu kuma sun tafi."
"Ko jirgi mai saukar angulun da aka tura yawo cikin daji bai gansu ba."

Yan bindigan da suka kai hari NDA sun bukaci N200m kudin fansa
Yan bindigan da suka kai hari NDA sun bukaci N200m kudin fansa Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Yan bindiga sun kai hari makarantar Soji NDA, sun hallaka Soja 2, sun sace 1

Wasu tsagerun yan bindiga sun kai mumunan hari makarantar horar da Sojin Najeriya NDA dake jihar Kaduna.

Rahoton ya nuna cewa yan bindigan sun hallaka mutum biyu yayinda suka yi awon gaba da jami'in Soja guda daya.

An tattaro cewa yan bindigan sun kai farmakin ne misalin karfe 1 na dare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel