Sunaye, maki da jihohi: Jerin dalibai 10 da suka zama zakaru a jarabawar JAMB na 2021

Sunaye, maki da jihohi: Jerin dalibai 10 da suka zama zakaru a jarabawar JAMB na 2021

  • Monwuba Chibuikem, dan asalin jihar Legas shi ne ya kasance zakaran da ya fi kowa maki a jarabawar shiga jami’ar shekarar 2021
  • A ranar Talata, hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’i ta sanar a taron da suka yi da minsitan ilimi, Malam Adamu Adamu
  • Chibuikem ya samu maki 358 bisa 400 wanda ya fi kowa maki, sai Qomarudeen Alabi dan jihar Osun da Adeogun Oreoluwa daga jihar Ogun suka samu maki 350 dukkan su

FCT, Abuja - Monwuba Chibuikem, dan asalin jihar Legas ya zama zakaran da ya fi kowa maki a jarabawar shiga jami’a ta UTME inda ya ke da maki 358.

Hukumar shirya jarabawar (JAMB) ta sanar da wannan labarin yayin taron da suka yi da ministan ilimi, Adamu Adamu a ranar Talata.

Kamar yadda wata takarda wacce The Cable Lifestyle ta gani ta bayyana, Qomarudeen Alabi daga jihar Osun da Adeogun Oreoluw daga jihar Ogun sun kasance na biyu inda suka samu maki 350 cif.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Kotu ta kori Gwamna Buni a matsayin shugaban riko na APC, ta dakatar da taron karamar hukuma

Sunaye, maki da jihohi: Jerin dalibai 10 da suka zama zakaru a UTME 2021
Hukumar JAMB ta saki sunaye, jihohi da makin dalibai 10 da suka fi cin jarabawar UTME ta bana. Hoto daga FUTA
Asali: Facebook

Ajayi Isaiah daga jihar Legas ya zama na hudu ya samu maki 349 sai kuma wani Okarike Kenneth daga jihar Rivers ya zama na biyar inda ya samu maki 348.

Daga nan Omonona Victor daga jihar Oyo, Owoeye Oluwatimilehin daga jihar Ekiti da Ehizogie Aidelogie na jihar Edo suka zama na shida da maki 347 yayin da Ajeigbe Samuel daga jihar Ekiti da Yakubu Joshua daga jihar Edo suka samu maki 345 da 343, inda suka kasance dalibai goma da suka fi kowa maki.

Zakarun guda goma da sunansu ya bayyana, tara daga cikin su maza ne sannan daya tak a cikinsu ce mace.

Bayanan sun nuna cewa mutane 5 na sama sun zabi jami’ar Covenant a matsayin jami’ar da suka zaba a farko.

Kara karanta wannan

Za mu hadu a kotu, Ortom ga Akume kan zargin dankara masa karya

Obafemi Awolowo University (OAU), jami’ar Legas (UNILAG), jami’ar Afe Babalola, Ado-Ekiti (ABUAD), jami’ar tarayya ta noma da ke Abeokuta (FUNAAB) da jami’ar Nnamdi Azikwe (UNIZAK), Awka inda kowanne cikinsu ya nemi daya daga cikin jami’o’in.

Sannan yawancin su sun nemi fannin kimiyya da fasaha ne.

The Cable ta ruwaito yadda hukumar jarabawar ta bar ko wacce jami’a ta yanke makin da dalibai za su kawo kafin ta basu gurbi a karo na farko cikin shekaru 43.

'Yan banga sun bindige mai garkuwa da mutane yayin da ya je karbar kudin fansa

A wani labari na daban, 'yan sandan jihar Adamawa sun tabbatar da sheke wani mai garkuwa da mutane da 'yan banga suka yi yayin da ya je karbar kudin fansa daga 'yan uwan wacce ya sace, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Sulaiman Nguroje, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a ranar Laraba a Yola, ya ce lamarin ya faru a ranar 26 ga watan Augusta a karamar hukumar Song ta jihar.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun fasa coci, sun yi awon gaba da masu ibada

Rundunar 'yan sandan jihar ta samu rahoto daga 'yan sandan Song a ranar 26 ga watan Augusta kan cewa 'yan banga sun sheke wani da ake zargi da garkuwa da mutane yayin karbar kudin fansa," Nguroje ya ce.

Asali: Legit.ng

Online view pixel