Za mu hadu a kotu, Ortom ga Akume kan zargin dankara masa karya
- Gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwai ya ce zai maka ministan ayyuka na musamman da harkokin gwamnati, Sanata George Akuma a kotu
- Gwamnan ya fadi hakan ne a ranar Laraba inda ya ce ya na bukatar Akume ya kawo gamsassun hujjoji zuwa kotu bisa tarin zargin da ya ke yi wa gwamnatinsa
- Dama Akume ya shawarci EFCC da ICPC su binciki duk wasu kudaden da gwamnatin tarayya ta narka da jihar Binuwai kama daga 29 ga watan Maris ta 2015 zuwa yanzu
Makurdi, Benue - A ranar Laraba, Gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom ya lashi takobin maka ministan ayyuka na musamman da harkokin gwamnati, Sanata George Akume a kotu don ya kawo hujjoji kwarara a kan zargin da ya ke yi wa mulkinsa.
Daily Trust ta ruwaito cewa, Ortom ya yi wannan furucin ne yayin tattaunawa da manema labarai a Makurdi inda ya zargi ministan da lailayo karya ya na maka masa a wata hira da aka yi da shi a Abuja.
Akume ya shawarci EFCC da ICPC inda yace su yi bincike mai tsanani a kan gaba daya dukiyar da gwamnatin tarayya ta bai wa jihar Binuwai tun daga 29 ga watan Mayun 2015 zuwa yanzu.
Ya kuma bayyana takaicinsa a kan yadda kullum Ortom ya ke sukar Shugaban kasa Muhammadu Buhari sannan ya nemi ya bai wa Buhari hakuri, TheCable ta ruwaito.
“Zan maka Akume a kotu don ya zo ya kawo gamsassun hujjoji a kan abubuwan da yake zargina da su. Ban yi wani abinda ya saba wa doka ba. Sai ya je ya yi bayani a kan karairayin da ya maka min a kotu,” a cewar Ortom.
Gwamnan ya ce, wadanda suka zabi Akume har sau biyu a matsayin gwamna sannan kuma sau 3 a matsayin sanata bai yi musu aikin komai ba, hasalima daba musu wuka yayi a bayansu.
Sannan shugaban jam’iyyar PDP na jihar Binuwai, ya soki wadannan zantukan na ministan.
Shugaban jam’iyyar, John Ngbede, a wata tattaunawa da yayi da manema labari, ya ce:
“Bukatar Sanata Akume ta dakatar da gwamnatin jihar Binuwai abin Allah wadai ne. Hakan na nufin a rushe duk wata kujerar siyasa a kuma nada wasu wadanda za su dinga bin umarninsa.
“Wadanda yake so a nada a kujeru yana so su bashi damar cin karensa babu babbaka kamar yadda yayi a kwanakin mulkinsa na karshe a 2007 lokacin da ya bar gidan gwamnati da mota cike da naira biliyan 2.
“Ya ga aljihunsa babu labari saboda yanzu ministan ayyuka na musamman ne shi, shiyasa ya ke neman yadda zai yi ya samu rabonsa a kudin gwamnatin jihar. Ya nemi makamancin hakan a 2007 lokacin gwamna Gabriel Suswam, sannan ya nemi hakan a 2015 a kan Gwamna Samuel Ortom.”
ISWAP ta yi ikirarin sheke sojin Najeriya 10, sace makamai da alburusai a Rann
A wani labari na daban, mayakan ta'addanci na ISWAP wadanda ake kira da Boko Haram, sun yi ikirarin sheke sojojin Najeriya goma bayan farmakin da suka kai sansanin sojojin da ke Rann, hedkwatar karamar hukumar Kala-Balge ta jihar Borno.
'Yan ta'addan ISWAP sun kai wa sojoji farmaki a garin da wuraren da aka sani da tallafin jama'a ta bangare daban-daban da yawansu a ranar Litinin.
A wata takardar da Daily Nigerian ta samu daga kungiyar 'yan ta'addan, ta ce ta kashe sojojin Najeriya goma tare da raunata wasu.
Asali: Legit.ng