Kano: Gobara ta lamushe rayuka 20, ta lashe kadarorin N5.6m

Kano: Gobara ta lamushe rayuka 20, ta lashe kadarorin N5.6m

  • Hukumar kwana-kwanan jihar Kano ta ce mutane 20 ne suka rasa rayukansu sakamakon gobara a jihar a watan Augusta
  • A cewar hukumar, an yi asarar dukiyoyi wadanda za su kai naira miliyan 5.6 duk a cikin watan da ya gabata
  • A ranar Laraba, jami’in hulda da jama’an hukumar, Saminu Abdullahi, ya bayyana hakan a wata takardar kiyasi

Kano - Hukumar kwana-kwanan jihar Kano ta ce an yi asarar rayukan mutane 20 da kuma dukiya mai kimar naira miliyan 5.6 sakamakon gobarar da aka yi a wurare daban-daban a fadin jihar cikin watan Augusta.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Saminu Abdullahi, jami’in hulda da jama’an hukumar ne ya bayar da wannan kiyasin a wata takarda a ranar Laraba a jihar Kano.

Kano: Gobara ta lamushe rayuka 20, ta lashe kadarorin N5.6m
Hukumar kwana-kwana ta jihar Kano ta bayyana kiyasin rayuka da kadarorin da aka rasa a watan Augusta. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

A cewar Abdullahi, hukumar ta samu nasarar ceton rayuka 102 da dukiyoyi da suka kai kimanin naira miliyan 14.7 sakamakon gobara 16 da ta auku a fadin jihar a cikin watan Augustan wannan shekarar.

Kara karanta wannan

Hotunan doya da fatanya da shugaban ƙaramar hukuma ta raba wa manoma a matsayin tallafi ya janyo maganganu

A cewarsa, hukumar ta amsa kiran gaggawa daga gidajen hukumar guda 27 da ke fadin jihar a cikin wannan lokacin, Daily Nigerian ta wallafa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Hukumar ta je wurare 81 bayan kiran ceton rai da aka yi mata da kuma kira 14 wadanda ba gaskiya bane daga mutanen jihar,” a cewarsa.

Abdullahi ya alakanta mafi yawan gobarar da rashin kulawa wurin amfani da wutar gas wurin girki da kuma gobara sakamakon wutar lantarki.

Ya shawarci mazauna yankin da su dinga kulawa don gudun barkewar gobara.

Ya kara da shawartar iyaye akan su tabbatar sun dakatar da yaransu daga yin iyo a rafuna a halin yanzu kuma su kula da inda zasu dinga zuwa.

Gwamnatin Niger ta rufe kasuwannin shanu, ta takaita yawo a babura

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Neja ta dakatar da cin kasuwar shanu ta kowanne mako a fadin jihar a matsayin hanyar magance hauhawar fashi da makami da kuma garkuwa da mutane.

Kara karanta wannan

Hoton Mutumin Da Kotu Ta Yanke Wa Hukuncin Ɗaurin Gidan Yari Bayan An Kama Shi Yana Satar Doya

Daily Trust ta ruwaito cewa, dokar za ta fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Satumban 2021.

Sakataren gwamnatin jihar, Ahmed Ibrahim Matane, ya bayyana wannan sanarwar ne ta wata takarda ta ranar Talata inda ya ce wajibi ne duk wani abin hawa da ke dauke da shanu da zai shiga cikin jihar ya nuna takardar shaida da alamar inda aka siyo shanun da kuma inda za a kai su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: